PDP: Shure–shure ba ya hana mutuwa
Mafi yawan ‘yan Najeriya, ba su fatan a samu maslaha a rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar jam’iyyar PDP. Mafi yawan mutanen Najeriya, za su so a ce Jam’iyyar PDP ta ci gaba da samun matsala; domin har yanzu mafi yawan ‘yan Najeriya ba su manta abubuwan da suka wakana shekara guda da ta […]
Mafi yawan ‘yan Najeriya, ba su fatan a samu maslaha a rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar jam’iyyar PDP. Mafi yawan mutanen Najeriya, za su so a ce Jam’iyyar PDP ta ci gaba da samun matsala; domin har yanzu mafi yawan ‘yan Najeriya ba su manta abubuwan da suka wakana shekara guda da ta wuce ba.
Wani abin da ya kara sanya ‘yan Najeriya kin jinin PDP shi ne, yadda suka kinkimo mai bunu a gindi domin ya zo ya kashe wutar rikicin da ke cin su. Shi ne tsohon Gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sherif, wanda masoyansa ke yi wa kirarin da cutar nan ta SAS. Da yawanmu sabon shugaban jam’iyyar yana tada hami ne kawai; muna tuna bakin mulkin shi na shekaru 8 a Barno da abin da hakan ya jawo ma Arewacin Najeria. Kowa ya san kafin Ali Modu Sherif ya zama Gwamnan Barno, akwai zaman lafiya sosai , to amma lokacin da ya zo, da siyasarsa ta ‘a mutu ko ai rai’ wadda ya kirkiro da ‘yan ta’addar siyasa na ECOMONG, wadanda wasu masana ke tunanin su ne ma suka rikize suka zama ‘Yan Boko Haram,kuma suka aika da dubu daruruwan mutane kiyama,kazalika,suke ci gaba da aika ta’asarsu labara ya ci gaba da sauyawa.
Ali Sherif yana tuna ma mu kawai dab akin ciki da bacin rai,da abubuwan da suka faruwa a 2009 zuwa 2011, a lokacin kazancewar rikicin Boko Haram. Masana harkar tsaro sun dangantaka kazancewar rikicin Boko Haram da matakan da aka dauka tsakanin wadannan shekaru. Amma don rashin sanin ya kamata da kuma cewa jam’iyyar PDP babu wani darasi da take koyo cikin al’amurranta ta rasa wanda za ta dauko sai wannan mutumen dad a yawa ‘Yan Arewa kema sa kallon makiyansu wanda keda hannu lalacewar yankin.
daya daga cikin dalilan da suka kashe jam’iyyar akwai rashin dimokuradiyya ta cikin gida. Kada mu manta da zaben kungiyar gwamnoni, wanda Rotimi Amechi ya kada Jonah Jang, to amma rashin dimokuradiyya ya sa suka ki karbar sakamakon abin da ya yi sanadiyyar ida rusa jam’iyyar PDP.
Shin jam’iyyar PDP ta yi nadamar cin amanar da tai ma Arewacin Najeriya, inda ta yi mursisi ta yi kememe, cewa, ita ba ta san da batun karba-karba ba, a cikinta? Saboda haka suka kwace wa Arewa hakkinta, sai ga shi yanzu don rashin kunya, wai su ne kan gaba wajen maganar karba-karba na mukamai, musamman abin da ya shafi shugabancin majalisa, inda suke goyon bayan Saraki da Dogara. Ire-iren wadannan munafunce-munafunce suna suka kai PDP suka baro,kuma za su ci gaba da yi mata tarnaki.
A lokacin PDP ne, ake shirya kasafin kudi,amma a ki aiwatar da shi, wai kuma don rashin kunya, har yanzu suna da bakin sukar Shugaba Muhammadu Buhari kan kasafin kudi. In kana ji ana a raba Najeriya gida-gida, to daga PDP nan ne matattarar barayin kasar nan, masu fasa bututun mai da yi wa arzikin kasa zagon kasa; masu garkuwa da mutane su ne ake baiwa kwangiloli; kudin da za a sai makaman tsaron kasa, su ne ake sacewa, sannan kuma wai a ce don me za a kama barayin da haka?
Yanzu Shugaba Muhammadu Buhari, duka-duka bai yi ko shekara daya bisa mulki ba, kuma ya dauko hanyar gyara, na sauya alkiblar tattalin arzikin mu daga mai dogara da danyen man fetur zuwa harkar noma da ma’adanai, ga batun kawo karshen dabi’ar amsar nagoro, abin da kasashe kamar na Sin suka runguma tun da dadewa, ga shi yana kokarin kawo karshen siyasar alfarma, kusan duk mutanen da yake nadawa,ba ubangida ya kawo su ba. Ga shi za a ga fannin tsaro yadda yake samun tagomashi, yanke-yanken ‘yan makaranta da talatanin dare, ko zagaye gari a kunna masa wuta, ko kunna wa kasuwa wuta, ko ka ga sojojin na tserewa daga filin daga, ko Shekau ya sako sakon bidiyo duk sun zama tarihi. To duk ire-iren wadannan matakai, wadanda sai an yi hakuri kafin a ci gajiyarsu, su ne makiyan kasar nan ba su so, shi ya sa suke ta kulle-kulle su ga cewa an mayar da kasar baya.
Bishir Dauda ya rubuto makalarsa daga Sabuwar Unguwa Katsina Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka na kasa 08165270879 [email protected]