PDP ta ƙi sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta Zaɓen Edo

Gwamnan jihar ya ce matuƙar aka cika waɗannan sharuɗa, za mu zo Abuja mu sanya hannu kan yarjejeniyar.

PDP ta ƙi sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta Zaɓen Edo

Jam’iyyar PDP ta ƙi sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Zaɓen Gwamnan Edo da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar da muke ciki.

Tsohon Shugaban Mulkin Sojin Nijeriya, Janar Abdulsalam Abubakar ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a wurin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a birnin Benin.

A cewarsa, PDP ta ce za ta amince ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne kawai idan har an cika wasu sharuɗa.

Ya bayyana cewar, “na gana da gwamnan jihar a jiya [Laraba] kuma ya shaida min cewar jam’iyyar PDP ba za ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba.

“Sai dai ya ce matuƙar aka cika waɗannan sharuɗa, za mu zo Abuja mu sanya hannu kan yarjejeniyar.”

Duk da cewar PDP da ɗan takararta a zaɓen, Mista Asue Ighodalo, ba su sa hannu a kan yarjejeniyar ba, sauran jam’iyyu ciki har da APC da ɗan takararta, Monday Okpebholo da takwaransa na jam’iyyar Labour, Olumide Akpata, sun rattaba hannu a kai.

Aminiya ta ruwaito cewa, shugabanni da ’yan takarar jam’iyyu 17 a zaɓen sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai Shugaban PDP, Dokta Tony Aziegbemi da ɗan takararta, Asue Ighodalo sun ki rattaba hannu.

Ana iya tuna cewa tun a Larabar da ta gabata ce Gwamna Godwin Obaseki ya ce babu lallai jam’iyyar PDP ta sanya hannu a kan yarjejeniyar.

Gwamnan ya faɗi haka ne tare da kafa hujjar cewa ayyukan ’yan sanda ya nuna cewa ba za su yi adalci ba illa iyaka jam’iyyar APC da suke bai wa fifiko.

Ya ce ’yan sanda da sa hannu jam’iyyar APC, sun kama aƙalla jiga-jigai 10 na jam’iyyar PDP waɗanda suke ganin za su taka rawar gani wajen tabbatar da nasarar jam’iyyarsu a zaɓen.

Game da hakan ne Gwamna Obaseki ya ɗiga ayar tambayar cewa ta yaya za su amince da yarjejeniyar zaman lafiyar da tun farko an nuna wariya da bai wa wata jam’iyya fifiko a kan sauran.

Shi ma shugaban jam’iyyar Azeigbemi ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar ba ta da wani tushe ballantana makama la’akari da cewa an kama tare da tsare mambobin jam’iyyar 10 a Abuja ba tare da gurfanar da su ba.

“Mun shirya wa wannan zaɓen, amma Babban Sufeton ’yan sanda ya fi kowane mutum nuna wariya a ƙasar nan.

“Ba za mu bari ya [Babban Sufeton ’yan sanda] wanda ba ɗan Jihar Edo ba ya tasiri a kan sakamakon zaɓen jihar.

“Muna kira da a janye duk wani ɗan sanda da ke shirin amfani da shi wajen ƙulla makirci a jihar.

A nasa ɓangaren, Babban Sufeton ’yan sandan, Kayode Egbetokun, ya ce ’yan sanda za su kasance masu gaskiya da tabbatar da ƙwarewar aiki don ganin an gudanar da sahihin zaɓe a jihar.

Ya buƙaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su rungumi yarjejeniyar zaman lafiyan hannu biyu tare da girmama duk wasu tsare-tsare da dimokuraɗiyya ta tanadar don an gudanar da sahihin zaɓe.