PDP ta ba fastoci Naira biliyan shida don su bata Buhari – Amaechi – PDP ta ce karya ne PDP ta ba fastoci Naira biliyan shida don su bata Buhari – Amaechi – PDP ta ce karya ne
Gwamnan Jihar Ribas kuma Darkta Janar na kamfen din dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, Mista Rotimi Amaechi ya yi zargin cewa Jam’iyyar PDP mai mulkin kasarb nan ta ba fastoci daban-daban a sassan Najeriya kimanin Naira biliyan shida domin su bata Janar Buhari a wurin mabiyansu. Gwamna Rotimi Amaechi […]
Gwamnan Jihar Ribas kuma Darkta Janar na kamfen din dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, Mista Rotimi Amaechi ya yi zargin cewa Jam’iyyar PDP mai mulkin kasarb nan ta ba fastoci daban-daban a sassan Najeriya kimanin Naira biliyan shida domin su bata Janar Buhari a wurin mabiyansu.
Gwamna Rotimi Amaechi ya bayyana haka ne a wurin taron yakin neman zaben Jam’iyyar APC da aka gudanar a karamar Hukumar Emohua da ke Jihar Ribas a ranar Talatar da ta gabata.
Cif Rotimi Amaechi ya ce bai kamata a ce an maida wuraren bauta wajen adawar siyasa ba.
Gwamna Amaechi ya kara da cewa, farstocin suna shaida wa mutane cewa wai idan Janar Buhari ya ci zabe zai mayar da kasar nan kasar Musulunci.
Cif Amaechi ya ce sharri ne kawai da bakar adawa ta Jam’iyyar PDP, ya sa take cewa Buhari zai musuluntar da Najeriya, ya ce in ba haka ba ta ina ne za a ce wani zai maida kasar nan kasar Musulunci.
Ya kara da cewa Jam’iyyar PDP ta sani cewa mutanen kasar nan sun waye kuma sun san irin wadannan karerayi na fakewa da addini don a bata jama’a.
Ya yi kira ga ’yan uwansa Kiristocin Najeriya cewa duk wani fasto da ya ce musu kada su zabi Janar Buhari saboda zai musuluntar da Najeriya, su ce ya maida wa kasa kudin talakawa da aka ba shi.
Sai dai kuma jam’iyyar PDP ta bakin kakakinta Olisa Metu ta karyata zargin da gwamnan ya yi, inda ta ce Amaechi yana kokarin zubar wa fastoci da mutuncinsu ne, ‘Amaechi yana bukatar addu’a’’ inji PDP.