PDP ta bukaci a yi zaben adalci bayan ta daga wa Obaseki kafa

Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP ya buƙaci a yi gaskiya a zaɓen jam’iyyar na fitar da ɗan takarar gwamnan jihar Edo, bayan ta amince gwamna Godwin Obaseki ya shiga takarar a ranar da ya koma jam’iyyar. Shugaban Kwamitin, Sanata Walid Jibril ya ce kwamitininsa ya amince da sassaucin Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar ta yi wa Gwamnan […]

PDP ta bukaci a yi zaben adalci bayan ta daga wa Obaseki kafa

Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo

Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP ya buƙaci a yi gaskiya a zaɓen jam’iyyar na fitar da ɗan takarar gwamnan jihar Edo, bayan ta amince gwamna Godwin Obaseki ya shiga takarar a ranar da ya koma jam’iyyar.

Shugaban Kwamitin, Sanata Walid Jibril ya ce kwamitininsa ya amince da sassaucin Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar ta yi wa Gwamnan koma za su yi aki tare da dukkan bangarori domin sake kafa gwamnati a Jihar Edo kuma.

“Ina kira ga dukkan ɓangarorin jam’iyya su ba Obaseki hadin kai jam’iyyarmu ta samu nasara saboda idan ya ci zaben dan takarar to damar PDP ta karu na sake kafa gwamnati a Edo da ma Najeriya”.

Da yake sanar da sassaucin, Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce Kwamitin Zartarwan jam’iyyar ya ɗaga wa Obaseki ƙafa ne kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya yi tanadi.

“Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa ya amince da buƙatar shugabannin dukkanin matakai a Jihar Edo na ɗaga wa Gwamna Obaseki ƙafa ya shiga zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP”, inji shi

Jam’iyyar ta kuma ɗage ranar zaɓen zuwa 25 ga watan Yuni a abin da ake ganin ƙoƙarin samun daidaito ne tsakanin Obaseki da sauran masu neman takara.

A ranar 19 ga wata Yuni ne Obaseki ya koma PDP ta kuma daga masa kafa ya nemi takara, kwana biyu da ficewarsa daga jam’iyyar APC bayan ta hana shi neman tsayawa takara a zaɓen gwamnan da ke tahowa.

Shigowarsa PDP wadda ke shirin zaɓenta a cikin mako guda ya zo a ƙurarren lokaci da kundin tsarin jam’iyyar bai zai bari ya nemi takara ba, sai idan ya samu sassauci daga Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa, wanda yanzu ya samu.

Tun sadda alamu suka tabbata cewa zai koma jam’iyyar, PDP ta ɗage zaɓen daga Juma’a 19 ga watan Yuni zuwa 23 ga watan, saboda abin da ta kira aikace-aikacen jam’iyya.

Bayan komawarsa, jam’iyyar ta sake ɗage zaɓen da karin kwana biyu bisa waɗannan dalilan.