PDP ta bukaci Buhari ya janye aniyarsa ta tsayawa takara a 2023

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci Muhammadu Buhari, da ya janye aniyarsa ta neman wa’adi na uku don tsayawa takara a zaben 2023, sannan ya yi amfani da sauran shekarun da suka rage masa akan mulki wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya. PDP ta soki fadar shugaban kasa game da shirin wanda zai gaji shugaba […]

PDP ta bukaci Buhari ya janye aniyarsa ta tsayawa takara a 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci Muhammadu Buhari, da ya janye aniyarsa ta neman wa’adi na uku don tsayawa takara a zaben 2023, sannan ya yi amfani da sauran shekarun da suka rage masa akan mulki wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

PDP ta soki fadar shugaban kasa game da shirin wanda zai gaji shugaba Buhari bayan wa’adinsa na biyu, inda suka ce, wannan koma baya ne ganin cewe bai yi shekara daya a wa’adinsa na biyu ba, amma an fara tunanin wanda zai gaji shugaban Najeriya.

Jam’iyyar PDP ta sanar da hakan ne a wani rahoto da Sakataren hulda da jama’a na kasa na PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar. Ya kuma ce jam’iyyar APC da fadar shugaban kasar ba tada alkibla a sauran shekaru uku masu zuwa.