PDP ta dakatar da Dino Melaye

An ɗauki matakin ne saboda rashin ɗa’a da cin zarafin jam’iyyar da ake zargin Melaye da aikatawa.

PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kogi ta dakatar da Sanata Dino Melaye bisa zargin cin amanar jam’iyyar.

Wannan mataki, a cewar wata takarda ta kwamitin gudanarwar jam’iyyar na gundumar Ayetoro/Iluagba Ward 1 ya yanke shi ne bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa domin bincikar laifukan da Melaye ya aikata.

A cewar shugabannin mazaɓar jam’iyyar, an ɗauki matakin ne saboda rashin ɗa’a da cin zarafin jam’iyyar da ake zargin Melaye da aikatawa.

Kwamitin zartarwa na mazaɓar jam’iyyar ne ya ɗauki matakin dakatar da shi a wani taro da ya gudana a unguwar Aiyetoro/Luagba Ward 1 ranar Juma’a.

Taron dai an yi shi ne domin duba rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa domin ya binciki zargin cin amanar jam’iyya da ake yi masa.

“Abin da Sanata Dino Melaye ya yi ya jawo wa jam’iyyar abin kunya da kuma tozarta da jam’iyyar kuma ba za a amince da ya ci gaba da zama a jam’iyyar ba.

“Saboda haka, shugabannin na Jam’iyyar mazaɓar ta dakatar da Dino Melaye daga Jam’iyyar PDP, nan take.

“Dakatarwar ta zo daidai da tanadin sashe na 59 (1) na kundin tsarin mulkin PDP wanda ya bai wa mazaɓar jam’iyyar ikon ɗaukar matakin ladabtarwa a kan mambobin da suka aikata irin wannan kuskure,” in ji ƙudurin.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra