PDP ta dakatar da Wamakko
Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar PDP ya dakatar da Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda daga jam’iyyar saboda zarginsa da saba wa dokokin jam’iyyar.Mai magana da yawun jam’iyyar Olisah Metuh ne ya sanar da dakatarwar a ranar Larabar da ta gabata, inda kuma ya ce an dakatar da gwamnan ne bayan wata ganawa da Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar […]
Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar PDP ya dakatar da Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda daga jam’iyyar saboda zarginsa da saba wa dokokin jam’iyyar.
Mai magana da yawun jam’iyyar Olisah Metuh ne ya sanar da dakatarwar a ranar Larabar da ta gabata, inda kuma ya ce an dakatar da gwamnan ne bayan wata ganawa da Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar ya yi a ranar Larabar.
Metuh ya ce: “Kwamitin ya tattauna kan dukkan abubuwan da suka shafi jam’iyyar da kuma mambobinta, sannan kwamitin ya samu Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko da laifin saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar karo da dama.
“Kwamitin ya ce Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya ki amsa gayyatarsa da kuma umarnin da kwamitin ya yi masa karo da dama, daga nan ya ci gaba da kin bin umarnin jam’iyya.
“Sakamakon hakan da kuma rashin amsa gayyatar kwamitin bayan ya bukaci ya bayyana a gabansa Laraba 5 ga watan Yuni, 2013 ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, don haka bisa karfin iko da kwamitin yake da shi daga kundin tsarin mulkin jam’iyyar sashi na 57 (3) da 57 (7) da 58. 1(c ),(h), (f) da kuma 59 (1),(2), ya dakatar da Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko daga jam’iyya, a yanzu kuma za a tura batunsa wurin kwamitin ladaftarwa na jam’iyyar.”
Ya ce, kwamitin ya yanke wannan hukuncin ne don tabbatar da bin doka da oda da kuma ladabi da biyayya a kowane mataki a cikin jam’iyyar.