PDP ta gwasale Jalo kan neman Jonathan ya yi magana game da Badakalar Dasuki
Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Mista Uche Secondus ya nesanta jam’iyyar daga bayanan da suke cewa jam’iyyar ta nemi tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fito ya yi magana game da badakalar karkatar da kudin sayo makamai na Dala biliyan biyu da miliyan 100 da ake kira da Badakalar Dasuki.Akwai manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP […]
Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Mista Uche Secondus ya nesanta jam’iyyar daga bayanan da suke cewa jam’iyyar ta nemi tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fito ya yi magana game da badakalar karkatar da kudin sayo makamai na Dala biliyan biyu da miliyan 100 da ake kira da Badakalar Dasuki.
Akwai manyan ’ya’yan Jam’iyyar PDP da dama cikinsu har da tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki da suke hannun Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) kan zargin da hannunsu a wannan badakala.
Mataiamkin Sakataren Labarai na Jam’iyyar Alhaji Abdullahi Jalo a kwanakin nan ya kira taron manema labarai inda ya bukaci Jonathan ya yi bayani kan da’war da Dasuki ya yi cewa an raba wadannan kudi bisa umarnin tsohon Shugaban kasar.
Sai dai Mista Secondus ya ce Jalo ya yi maganar ce a madadin kansa amma wannan ba shi ne matsayin shugabannin Jam’iyyar PDP ba.
“Bari in fada muku balo-balo cewa Jalo yana bayyana ra’ayinsa ne kawai, kuma ra’ayinsa ba yana nuna matsayin jam’iyya ba ne. Babu wani lokaci da muka zauna a Kwamitin Zartarwa na kasa muka tattauna cewa ya kamata Jonathan ya yi magana kan badakalar sayo makaman. Babu lokacin da aka kawo wannan batu. Don haka Jalo yana bayyana ra’ayinsa ne,” inji Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar.
Ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar ta kasa Cif Olisa Metuh da sauran jiga-jigan jam’iyyar da Hukumar EFCC ke yi.
Alhaji Jalo ya shaida wa manema labarai cewa a ranar Asabar cewa wajibi ne tsohon Shugaban kasa Goodluck ya yi wa ’yan Najeriya da kuma jama’ar duniya bayanin kana bin da ya sani game da batun.
Jalo ya ce, “Kamar yadda kuka sani babu sisin kwabo da Gwamnatin Tarayya za ta kashe ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ta kasa ba. Kudin da aka ware domin sayo makamai wadansu mutane sun karkatar da su zuwa wani abu daban. Mutane da dam da ba a zato suna da hannu a ciki, yanzu haske ya bayyana duhu yay aye.”
Ya kara da cewa: “Jonathan yana raye don haka wajibi ne ya yi bayani ko shi ya ce wa Mashwarcinsa kan Tsaro ya sauya wa kudin da aka ware don yaki da Boko Haram zuwa yi masa kamfe. Na fito daga Arewa maso Gabas ne na san mugun halin rashin zaman lafiya da jama’armu ke fuskanta a can. An ware kudin ne don yaki da Boko Haram, kuma mun san ba za ka iya mulki ba idan ba zaman lafiya. Mu ba wawaye ba ne. Kudin da aka ware don kamfe an mika ne wa shugaban jam’iyyarmu ba.”
Jalo ya ce ya ji dadi da wadanda suka karbi wannan kudi babu wanda ya ce ya karba ne a madadin Jam’iyyar PDP.