PDP ta kwace kyautar tiransifoma bayan ta sha kaye a Jihar Oyo

Da sanyin safiyar Asabar da ta gabata, sabuwar na’urar lantarki (transformer) da dan takarar kujerar gwamna na jam’iyar PDP a Jihar Oyo, Sanata Teslim Folarin, ya bayar kafin ranar zabe domin amfanin mazauna unguwar Sabo cikin birnin Ibadan ta yi layar zana. Daga baya an gano cewa, wakilan Sanata Teslim Folarin ne suka dauke wannan […]

PDP ta kwace kyautar tiransifoma bayan ta sha kaye a Jihar Oyo
PDP ta kwace kyautar tiransifoma bayan ta sha kaye a Jihar Oyo

Da sanyin safiyar Asabar da ta gabata, sabuwar na’urar lantarki (transformer) da dan takarar kujerar gwamna na jam’iyar PDP a Jihar Oyo, Sanata Teslim Folarin, ya bayar kafin ranar zabe domin amfanin mazauna unguwar Sabo cikin birnin Ibadan ta yi layar zana. Daga baya an gano cewa, wakilan Sanata Teslim Folarin ne suka dauke wannan na’ura saboda mutanen unguwar ba su jefa masa kuri’u ba.

daruruwan mazauna unguwar Sabo a karkashin jagorancin Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, sun yi dafifi suna kallon ikon Allah a daidai wurin da aka ajiye wannan na’ura, a harabar babban masallacin unguwar. An dawo da wannan na’ura bayan awoyi 3 da dauke ta, sai dai a nan take jama’a suka ki amincewa da mayar da ita. Suka rika cewa, “ba ma so, ba ma so, a yi gaba da ita!”
Tsohon Kansila a karamar Hukumar Ibadan ta Arewa, Alhaji Bashir Mai Borno, shi ne ya girke wannan na’urar a harabar masallacin, a madadin dan takarar gwamna Teslim Folarin, mako daya kafin ranar zabe kuma shi ne ya dauke ta daga wurin da aka ajiye ta. Ya musanta cewa, rashin zaben Teslim Folarin da jama’a suka yi a unguwar Sabo ne ya sa suka kwace wannan na’ura.
Ya ce, “ko kusa babu abun da ya yi kama da haka, mun kawar da wannan na’ura daga wannan wuri ne domin samar da wani wuri daban domin guje wa barayi. Tun farko mun samu labarin cewa, akwai wasu mutane da suka yi yunkurin sayar da wannan na’ura a boye ga ainihin mutumin da aka saye ta a hannunsa, wanda ya ba mu labarin abun da ake ciki shi ne dalilin da ya sa muka dauki wannan mataki ba tare da sanin Sanata Teslim Folarin ba. Inji Bashir Mai Borno.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani a fadarsa, Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad dahiru Zungeru, ya ce, “yau da safe ne daya daga cikin mutane masu goyon bayan jam’iyar PDP ya zo ya dauke wannan na’ura daga wurin da aka ajiye ta a harabar babban masallacinmu, wanda a nan take jama’a suka ba ni labari. Ni kuma na je na gane wa idanu na komai. A binciken da na yi, na gano cewa, Alhaji Bashir Mai Borno shi ne ya zo da sassafe ya dauke na’urar saboda su nuna fushinsu ga jama’a da ba su jefa kuri’unsu ga Sanata Teslim Folarin a zaben da aka yi a jiya Asabar ba. A lokacin da aka dawo da na’urar bayan awoyi 3 da dauke ta na ki amincewa da sake karbar na’urar har sai mun ji cikakken bayani daga bakin mutumin da ya bayar da ita wato, Sanata Teslim Folarin domin muna son sanin ko shi ne ya aiko a dauke kyautar da ya yi mana ko kuwa wasu ne suke amfani da shi domin bata masa suna.”