PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun

Hukumar Zaɓen Osun OSSIEC ta ce an samu nasarar gudanar da zaɓen bisa duk wani tanadi na doka.

PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun

Zababben Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke da aka rantsar

Jam’iyyar PDP mai ci a Jihar Osun ta lashe zaɓen dukkan kujerun ƙananan hukumomin jihar guda 30 da na kansiloli 332 da aka gudanar yau Asabar.

Shugaban hukumar zaɓen jihar OSSIEC, Hashim Abioye ne ya sanar da sakamakon a wani taron ganawa da manema labarai da ya yi a jihar.

Da yake jawabi a yammacin wannan Asabar ɗin a birnin Osogbo, Hashim Abioye ya ce an samu nasarar gudanar da zaɓen bisa duk wasu tsare-tsare da dokoki suka tanadar.

Ya bayyana cewa jam’iyyu 18 ne suka shiga zaɓen domin cike giɓin da ake da shi a madafan iko na ƙananan hukumomin jihar guda 30.

Aminiya ta ruwaito cewa an samun takun saƙa tsakanin gwamnatin jihar da ’yan sanda da ma Ministan Shari’a na Nijeriya.

Ministan ya buƙaci a dakatar da zaɓen, sannan ’yan sanda suka ce sun samu bayanan sirri kan yiwuwar tayar da hargitsi, don haka suka yi kira ga gwamnan da ya dakatar da yunƙurinsa na gudanar da zaɓen, lamarin da shi kuma ya ce babu gudu, babu ja da baya.

PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu

An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines

Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana?