PDP ta lashi takobin lashe zaben kananan hukumomi a Gombe 

Jam’iyyar ta bayyana kwarin gwiwarta kan zaben da ke tafe.

PDP ta lashi takobin lashe zaben kananan hukumomi a Gombe 

Jami’yyar PDP Jihar Gombe, ta lashi takobin lashe zaben Kananan Hukumomi da za a gudanar a watan Afrilun 2024.

Shugaban jam’iyyar na Karamar Hukumar Nafada Yusuf Isa Jigawa ne, ya bayyana hakan a jihar.

Ya bayyana hakan ne a garin Nafada a yayin wata ziyara da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hayatu Usman, ya kai don ganawa da al’ummar yankin.

A cewarsa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar (GOSIEC), ta sanya watan Afirilu 2024 a matsayin lokacin da za a yi zaben.

Ya ce suna da kwarin guiwa ganin yadda jami’yyar ke kara samun karbuwa a jihar.

“A zaben sanatoci PDP na da biyu cikin uku, ’yan majalisu biyar cikin shida, hakan yana nuna karfin da jami’yyar nan ta ke da shi,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar a jihar, da su rungumi zaman lafiya domin don samun doka da oda.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja