PDP ta mayar da Wike dan kallo a kwamitin yakin neman zaben Atiku
Jam’iyyar ta nada Tambuwal a matsayin Darakta-Janar na kwamitin, wanda Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel ke jagoranta.
Jam’iyyar PDP ta nada Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal a matsaiyn Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Dan Takararta na Shugaban Kasa a zaben 2023, Atiku Abubkar.
Jam’iyyar ta nada Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a matsayin dan kallo a kuwamitin wanda Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ke shugabanta.
- Masarautar Jama’a ta tube rawanin Sarkin Yaki da Sarkin Fada
- Jiragen Yaki Sun Kashe Manyan Kwamandojin ISWAP A Tafkin Chadi
Sauran shugabannin kwamitin su ne Gwamnan Jihar Bauchi, a matsayin Mataimaikin Shugaba na Yankin Arewa, sai kuma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin daga yankin Kudu.
Sauran jagorin kwamitin gudanarwar yakin neman zaben na PDP (NCMC) su ne:
- Sanata Liyel Imoke — Mataimakin Darakta-Janar kan Ayyuka
- Farfesa Adewale Oladipo — Mataimakin Darakta_janar kan Gudanarwa
- Cif Raymond Dokpesi — Mataimakin Darakta-Janar Kan Aiki da Cikawa da Tsare-tsare
- Cif Okwesilieze Nwodo — Mataimakin Darakta-Janar kan Bincike da Tsare-tsare .
Daukacin gwamnonin jam’iyyar mambobi ne a kwamiti, ciki har da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda ke neman Shugaban Jam’iyyar, Sanata Iyorchia Ayu daga mukaminsa.
Sanarwar da Jam’iyyar ta fitar ta shafinta na Twitter, dauke da sanya hannun Sakataren Tsare-tsarenta na Kasa, Umar Mohammed Bature ta bayyana cewa ranar 28 ga watan Satumba, 2022 za a rantsar da mambobin kwamitin.