PDP ta nemi majalisa ta yi watsi da bukatar Buhari na karbo bashi
Jam’iyyar PDP ta nemi Majalisar Dokokin Najeriya da kada ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na karbo bashin Dala biliyan biyar da digo biyar daga kasashen waje. Jam’iyyar ta bayyana lamarin da wani mataki da jam’iyyar APC ta dauka don su jefa kasar cikin wani sabon bashi tare da sarayar da makomar kasar. A […]

Jam’iyyar PDP ta nemi Majalisar Dokokin Najeriya da kada ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na karbo bashin Dala biliyan biyar da digo biyar daga kasashen waje.
Jam’iyyar ta bayyana lamarin da wani mataki da jam’iyyar APC ta dauka don su jefa kasar cikin wani sabon bashi tare da sarayar da makomar kasar.
A sanarwa da Mai Magana da Yawun Jam’iyyar PDP, Prince Dayo Adeyeye ya sanya wa hannu jam’iyyar ta nemi APC ta bayar da bahasin dukkan kudaden da ta karbo tun lokacin da ta hau kan karagar mulki.