PDP ta sake ɗage babban taronta zuwa Mayun 2025

Ɗage taron ba zai rasa nasaba da rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta ba.

PDP ta sake ɗage babban taronta zuwa Mayun 2025

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa (NEC), zuwa ranar 15 ga watan Mayu, 2025.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, wanda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye, ya bayyana hakan.

Tun asali, an tsara gudanar da taron ne a ranar 13 ga watan Maris 2025, amma aka ɗage shi saboda wasu zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a jihohi daban-daban.

Tun a shekarar da ta gabata ne PDP ta tsara yin wannan babban taro karo na 98, amma ana ci gaba da ɗagewa.

Rahotanni na nuni da cewa matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta, kamar rikicin shugabanci da rashin daidaiton ra’ayi tsakanin manyan jiga-jiganta, na iya zama dalilin jinkirin.

Yanzu haka, ana sa ran taron zai kasance muhimmin mataki ga makomar jam’iyyar, musamman duba da shirye-shiryenta na fafatawa a babban zaɓen 2027.