PDP ta yi Allah-wadai da sace dalibai 200 a Kaduna

Maharan sun yi awon gaba da daliba sama da 200 a jihar.

PDP ta yi Allah-wadai da sace dalibai 200 a Kaduna

Shugabancin Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, ya yi Allah-wadai da sace daliban Firamare da Sakandare sama da 200 da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun.

Sakataren Yada Labaran PDP na Jihar, Abraham Catoh ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna.

Catoh, ya ruwaito shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Felix Hassan-Hyat ya yi kira ga sojoji da sauran jami’an tsaro da su hada kai wajen ceto daliban da shawo kan matsalar rashin tsaro da sauran ayyukan miyagun ayyuka a jihar.

“Jam’iyyar PDP na goyon bayan kudurin Gwamnan Jihar na ceto daliban ba tare da wani abu ya same su ba.

“Muna kuma kira ga gwamnan da kada ya bari a yi kasa a gwiwa wajen ceto wadannan yara da kuma dakile ayyukan ‘yan ta’adda da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

“PDP na tausaya wa iyayen da aka sace ‘ya’yansu,” in ji shi.

Idan za a tuna a makon da ya wuce ne wasu ‘yan bindiga suka shiga makarantun firamare da sakandare tare da yin awon gaba da dalibai da wasu malamai.