PDP ta yi wa Buhari ta’aziyya
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana juyayinta kan rasuwar dan jarida kuma attajiri, kuma tsohon minista kuma atttajiri, Malam Isma’ila Isa Funtua. PDP ta bayyana haka ne sakonta na ta’aziya ga Shugaba Buhari, wanda mamacin babban makusancinsa ne tsawon lokaci. “PDP na ta’aziyya ga iyalan Malam Sama’ila Isa Funtuwa da ‘yan jarida da kuma al’umma […]
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana juyayinta kan rasuwar dan jarida kuma attajiri, kuma tsohon minista kuma atttajiri, Malam Isma’ila Isa Funtua.
PDP ta bayyana haka ne sakonta na ta’aziya ga Shugaba Buhari, wanda mamacin babban makusancinsa ne tsawon lokaci.
“PDP na ta’aziyya ga iyalan Malam Sama’ila Isa Funtuwa da ‘yan jarida da kuma al’umma da gwamnatin jihar Katsina, tare da rokon Allah Ya yi masa rahama”, inji jam’iyyar.
Sakataren Yada Labaran jam’iyyar Kola Ologbondiyan a cikin sanarwar, ya yaba da irin gudunmuwar domin ci gaban Najeriya a lokacin rayuwarsa.