PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

PDP ta ce jami’yyar APC na shirin jega dimokuraɗiyyar Najeriya cikin hatsari.

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Edo, tare da bayyana ƙudirinta na garzayawa kotu don ƙalubalantar sakamakon.

A wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja, Shugaban riƙo ƙwarya na jam’iyyar PDP, Ambasada Umar Damagum, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta sake duba sakamakon zaɓen.

Ya ce ya kamata INEC ta sanar da sakamakon gaskiya da ya fito daga ƙuri’un da jama’ar jihar suka kaɗa a rumfunan zaɓe.

Damagum, ya yi ikirarin cewa mutanen Edo sun zaɓi ɗan takararsu, Dokra Asue Ighodalo, amma an yi maguɗi a sakamakon zaɓen don bai wa jam’iyyar APC nasara.

Ya ce zaɓen ya kasance cike da tashin hankali, tsoratarwa, da kuma cushen ƙuri’u.

Ya jaddada cewa yadda kotu za ta gudanar da shari’a game zaɓen ne kaɗai zai nuna ko har yanzu akwai adalci a Najeriya.

A cewarsa, idan tsarin shari’a ya gaza, Najeriya na cikin hatsari.

Damagum, ya kuma zargi jam’iyyar APC da haɗa kai da jami’an INEC da kuma jami’an tsaro don yin katsa-landan a zaɓen.

Ya ce matuƙar aka bari irin haka na ci gaba da faruwa, dimokuraɗiyyar Najeriya na cikin hatsari.