PDP ta zabi Saraki jagoran yakin neman zaben Atiku

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta zabi shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban Najeriya 2019. Yayin aka zabi Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwar a matsayin shugaban yakin neman zaben na shiyyar Arewa maso Yamma. Sakataren jami’iyyar PDP na kasa Kola Ologbondiyan ne ya […]

PDP ta zabi Saraki jagoran yakin neman zaben Atiku

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta zabi shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban Najeriya 2019.

Yayin aka zabi Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwar a matsayin shugaban yakin neman zaben na shiyyar Arewa maso Yamma.

Sakataren jami’iyyar PDP na kasa Kola Ologbondiyan ne ya sanar da hakan yau Talata a Abuja, yayin da Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo zai shugabanci yakin neman zaben a yankin Arewa maso Gabas.