PDP ta zabi shugabanninta a Jihar Kano

Jam’iyyar PDP ta gudanar da zaben shugabanninta a Jihar Kano, domin jan ragamarta tare da gudanar da al’amuranta. An gudanar da zaben ne a gidan silima na Marhaba inda aka kwana har zuwa wayewar gari, a zaben da wakilai sama da dubu suka kada kuri’a.Zaben ya biyo bayan gazawar kokarin masalaha ne wajen fitar da […]

PDP ta zabi shugabanninta a Jihar Kano
PDP ta zabi shugabanninta a Jihar Kano

Jam’iyyar PDP ta gudanar da zaben shugabanninta a Jihar Kano, domin jan ragamarta tare da gudanar da al’amuranta. An gudanar da zaben ne a gidan silima na Marhaba inda aka kwana har zuwa wayewar gari, a zaben da wakilai sama da dubu suka kada kuri’a.
Zaben ya biyo bayan gazawar kokarin masalaha ne wajen fitar da shugabannin, sakamakon bangarorin da suka tada jam’iyyar a halin yanzu.
Sakamakon zaben ya nuna cewa Alhaji Rabi’u dansharu wanda ake jin dan takara ne na tsohon mashawarcin Shugaban kasa, Alhaji Akilu Indabawa, ya samu kuri’a 1,109 inda ya doke abokin takararsa daga bangren Ministan Harkokin Waje, Alhaji Aminu Wali, tsohon Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, wanda ya samu kuri’a 458.
Bayan kammala zaben ana ganin kowane gida daga gidajen bangarorin jam’iyyar a Jihar Kano ya samu nasa kason mukami, inda gidan tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya samu mukamin Sakatare.