PDP-’Yar Dubai ta kayar da Mai Farin Gilashi
Litinin, 20 ga Janairu, 2014 mahukuntan jamiyyar ta PDP suka zakulo wani jigo a jamiyyar wanda ya shafe shekaru 8 a matsayin gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar Jamiyyar ta PDP, wato Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu (Walin Bauchi), hasashe na nuna cewar, tsugune dai ba ta kare ba, domin tarihi ya nuna, an taba samun […]
Litinin, 20 ga Janairu, 2014 mahukuntan jamiyyar ta PDP suka zakulo wani jigo a jamiyyar wanda ya shafe shekaru 8 a matsayin gwamnan jihar Bauchi a karkashin inuwar Jamiyyar ta PDP, wato Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu (Walin Bauchi), hasashe na nuna cewar, tsugune dai ba ta kare ba, domin tarihi ya nuna, an taba samun rabuwar kai yayin da Gwamna.Isah Yuguda ya koma jamiyyar sa ta PDP daga tsohuwar jam’iyyar ANPP bayan ya shekara biyu akan karagar mulkin jihar. Wannan tasa aka samar da tsohuwar PDP da lakabin ‘Yar-Dubai’ yayin da sabuwar kuma ke da lakabin Mai-Farin Gilashi.
Gwamna Isah Yuguda dai aboki ga Amadu, a yayin da ya taba tura shi ya wakilci Jihar Bauchin a matsayin Minista, amma abotar ta fara babewa ne yayin da Malam Isah Yuguda ya so ya tsaya takarar gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP, wanda Adamu Mu’azu ya yi fur ya hana, wannan ta sa Isah Yuguda ya koma jam’iyyar Adawa a wancan lokacin ta ANPP, ya kuma lashe zaben..
Da dama jaridu da gidajen rediyon ciki da wajen kasar nan sun rawaito ire-iren tsamar da ke tsakanin gaggan biyu, duk da masana siyasa na cewa alakar su ta abota tana nan daram, amma kuma talakawan Jihar na musanta yiwuwar hakan.
Hukumar EFCC ta gayyaci Tsohon Gwamnan Mu’azu don amsa wassu tambayoyi akan almundahana da kudin Jihar ta Bauchi, a yayin da Majalisar Dokokin Jihar ta wancan lokacin ta yi dokar hana Tsohon Gwamna Mu’azu rike duk wani mukami a Jihar na tsawon shekaru 10.
Duk da cewar, wasu kafafen yada labarai na kasar nan sun rawaito cewar Gwamna Yuguda ne ya mika sunan Adamu Mu’azu don ya zamto Shugaban PDP, wadansu majiyoyin na karyata yiwuwar hakan, hasali ma dai an ce, Malam Isah Yugudan ya nuna kin amincewar sa da zabar Alhaji Adamu Mu’azun.
A wata ruwayar, Shugaba Jonathan ya zabi Mu’azu ne ba don komai ba, sai don irin alakar Isa Yuguda da surikinsa, wato Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa dangane da irin halin da aka nuna masa lokacin da marigayin ke kwance a asibiti, yayin da ake hana Jonathan samun ganawa da marigayin, wanda aka ce, su Gwamna Isha Yuguda ke da alhakin hakan.
Lallai akwai rina a kabar siyasar jihar mu ta Bauchi, kowa (Muazu da Yuguda) zai so nuna bajintar sa, don samun mabiya a jam’iyyarsu ta PDP, wanda hakan shi zai jawo rashin jituwa a tsakanin gaggan biyu.
Fatan mu Adamu Mu’azu da ka yi hakuri da wannan aboki naka ku tafi tare, har zuwa karshen mulkin sa a 2015, kada ka barshi ya canza jam’iyya. Kai kuma Malam Isah Yuguda, tunda muka zabe ka a Jamiyyar adawa kuma ka gudu ka barmu, to kada kayi sha’awar dawo wa sabuwar jam’iyyar mu ta APC, don babu kofar karbar ka. Juyin juya halin da ya kawo ka, shi ne kuma zai cire ka da duk masu goya maka baya.
Haka zalika, kamar yadda Alhaji Bamanga Tukur ya taimaka wajen samar wa da kuma karfafa jam’iyyar adawa ta APC a Najeriya, haka kaima (Mu’azu) muna sa ran za ka yi mana abin da yafi haka, mu a wurin mu Bamanga Tukur ya iya mulki sosai, kuma irin sa ake bukata musamman a jam’iyyar PDP don karasa tarwatsa ta da rusa ta. Haka kuma shi ne zai kai mu ga nasarar Baba Buhari ya karbi mulkin kasar nan a 2015, da fatan za ka gaji abin da Alhaji Bamanga Tukur ya yi mana.
Muna yi wa Alhaji Adamu Mu’azu fatan alheri, da fatan ba za su shafa maka kashin kaji ba, kada ka gagara aiwatar da aikin karasa rusa wannan jam’iyya ta PDP da ta hana kasar nan ci gaba.
Muna fatan Tsawon rai, Jamiyyar APC da Jihar Bauchi da Tarayyar Najeriya
Salisu Dango Yana, K/H Shira Jihar Buachi 2348032875677 [email protected], [email protected]