PDP za ta karbe Sakkwato da karfin tsiya – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa y ace Jam’iyyar PDP za ta yi amfani da karfin cin tuwo ta kwace mulki a jihar. Kuma ya ce bayan karbe mulkin za su daure Gwamnan Jihar Aliyu Magatakarda Wamakko. Bafarawa ya bayyana haka ne a wuril gangamin karshe na Jam’iyyar PDP a Sakkwato, inda ya musanta […]

PDP za ta karbe Sakkwato da karfin tsiya – Bafarawa
PDP za ta karbe Sakkwato da karfin tsiya – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa y ace Jam’iyyar PDP za ta yi amfani da karfin cin tuwo ta kwace mulki a jihar. Kuma ya ce bayan karbe mulkin za su daure Gwamnan Jihar Aliyu Magatakarda Wamakko.

Bafarawa ya bayyana haka ne a wuril gangamin karshe na Jam’iyyar PDP a Sakkwato, inda ya musanta rade-radin cewa an ba shi kudi ne ya koma PDP tare da bayyana cewa zai iya biyan ma’aikatan jihar albashi daga aljihunsa.
“Sun ce muna shirin yin magudi a zabubbuka masu zuwa a jihar; ban san me ya sa suke tsoron magudi bayan sun san cewa su ma ta hanyar magudi suka hau mulki. Bari in gaya musu za mu yi amfani da karfi da magudi da kuma kuri’unmu wajen korarsu daga mulki,” inji shi.
Tsohon Gwamnan ya ce a shekarar 2007, ya shaida wa mutane cewa za su yi da na sanin zaben Gwamna Wamakko, “Saboda shi baa bin amincewa ba ne. Lokacin Wamakko ya yi. Za mu karbe mulki ta kowace irin hanya,” inji shi.
Ya yi zargin cewa Gwamna Wamakko ya tafi kotu yana neman ta hana Hukumar EFCC da ICPC daga kama shi bayan ya bar mulki. “To amma kamar yadda shugaban jam’iyyarmu y ace, za mu tura shi kurkuku idan muka karbe mulki,” inji Bafarawa.
Mataimakin Gwamnan Jihar Mukhtari Shagari, ya ce PDP ce za ta lashe zaben jihar. Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar, Alhaji Ibrahim Milgoma ya ce, ba za su taba yafe wa Gwamna Wamakko ba, saboda shirya yadda za a daure jagoransu Bafarawa, kuma ya shirya wa haduwa da irin wannan abin da ya yi idan aka kayar da shi a zabe.
dan takarar Gwamnan Jihar na PDP Sanata Abduallah Wali, ya ce gwamnatinsa za ta sa kafar wando daya da duk wanda aka samu yana bangar siyasa a jihar. Kuma ya yi alkawarin inganta rayuwar matasa da mata idan aka zabe shi, kuma gwamnatinsa ba za ta yi almubazzaranci da kudin jama’a ba.
Sai dai a martaninta, Jam’iyyar APC ta yi watsi da da’awar tsohon Gwamnan. Kakakin Jam’iyyar na Jihar Sakkwato, Alhaji Sidi Aliyu ya ce Bafarawa ya rasa tagomashi, kuma ‘fanko ne a fagen siyasa.”
Game da barazanar daure Gwamna Wamakko, Sidi Aliyu Gwamnan bai aikata wani abu da za a yi masa haka ba, “Gwamna Wamakko bai saci kudi ko ya yi almubazzaranci da dukyiyar talakawa ba,” inji shi.