PDP za ta rasa ’yan Majalisa 11 a jihar Jonathan
A yayin da Jam’iyyar APC ta fara rajistar mambobinta a daukacin kasar nan a shekaranjiya Laraba, alamu masu karfi sun nuna ’yan Majalisar Jihar Bayelsa 11, watau jihar Shugaba Goodluck Jonathan, suna dab da ficewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Aminiya ta samu bayani daga wani jigon APC cewa ’yan majalisar ba su gamsu da […]
A yayin da Jam’iyyar APC ta fara rajistar mambobinta a daukacin kasar nan a shekaranjiya Laraba, alamu masu karfi sun nuna ’yan Majalisar Jihar Bayelsa 11, watau jihar Shugaba Goodluck Jonathan, suna dab da ficewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Aminiya ta samu bayani daga wani jigon APC cewa ’yan majalisar ba su gamsu da halin ko in kula da Gwamna Dickson ke nunawa game da zabe mai zuwa ba, inda suke tuntubar jam’iyyar APC a asirce. Kuma ya ce ’yan majalisar za su yi rajistar zama ’yan jam’iyyar da aka fara a shekaranjiya. Sai dai ya ki bayyana sunayen ’yan majalisar, inda ya ce yin hakan riga malam masallaci ne kuma don a kare su ne daga “mugun kullin” PDP. Akwai tsoron cewa ’yan majalisar wadanda aka zabe su tare da tsohon Gwamnan Jihar Mista Sylba har yanzu mafi yawansu suna yi masa biyayya. Wailinmu ya ruwaito cewa rajistar ’ya’yan Jam’iyyar APC a jihar yana samun gagarumar nasara, inda daruruwan magoya bayanta suka mamaye Sakatariyar Jam’iyyar suna rajista da ita. Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Tiwei Orunimighe, ya shaida wa magoya bayanta cewa PDP a jihar ta mutu an yi jana’izarta, inda ya ce APC za ta kwace mulki daga hannunta a jihar.