Pepe ya yi ritaya daga tamaula 

Cristiano Ronaldo, ya yi wa Pepe godiya a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Pepe ya yi ritaya daga tamaula 

Fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Pepe ya sanar da ritayarsa daga murza leda.

Cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Pepe mai shekaru 41 ya ce yana miƙa godiyarsa ga duk waɗanda suka goya masa baya a tsawon shekarun da ya shafe a fagen tamaula.

“Ina godiya ga kowa musamman ƙungiyoyin da na bugawa tamaula da kuma ƙasar Portugal.

“Na samu goyon bayan da nake buƙata kuma yanzu ina mai ajiye wannan sana’a zuciya cike da gamsuwa.

Pepe dai ta soma murza leda ne a ƙungiyar Maritimo da ke Portugal tun yana ɗan shekara 18, sannan daga nan ya zarce ƙungiyar FC Porto.

Zaƙaƙurin ɗan wasan bayan ya kuma buga wa Real Madrid da ke Sfaniya da kuma ƙungiyar Besiktas ta ƙasar Turkiyya.

Pepe ya shafe shekaru 10 yana murza leda a Madrid, inda ya lashe kofuna Gasar Zakarun Turai uku da Kofin Duniya na Ƙungiyoyi biyu da Kofin La Liga uku.

Tsohon abokin wasansa a Madrid da Portugal Cristiano Ronaldo, ya yi wa Pepe godiya a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram: “Babu wasu kalmomi da zan yi amfani da su da za su bayyana matsayinka a wurina abokina.

“Mun yi nasara kan duk abin da ya kamata mu samu a filin wasa tamaula, amma babbar nasara ita ce abota da girmamawar da nake muka. Kai na daban ne, ɗan uwa. Kuma ina godiya a gareka marar misali.”

A bayan nan ne Pepe ya kafa tarihin zama ɗan wasa mafi tsufa da ya haska a Gasar Kofin Nahiyyar Turai yayin da ya wakilci ƙasar Portugal a Euro 2024 yana da shekaru 41 a doron ƙasa.

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa na Portugal, Fernando Gomes, ya ce Pepe ya shiga rukunin ’yan wasan da babu kamarsu.

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta shiga ƙungiyar BRICS

Gwamnatin Kano ta haɗa gwiwa da Media Trust kan inganta harkokin yaɗa labarai