Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi

Ana sa ran idan sun kammala ganawar za su sanar da manema labarai abin da suka tattauna.

Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, na ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi.

Taron na gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, amma ba a bayyana manufarsa ba tukuna.

Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi.

Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed za su yi magana da ’yan jarida bayan kammala ganawar tasu.

Wannan ganawa na faruwa ne a daidai lokacin da ’yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Obi ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya lashe.