Peter Obi ya kusa dawowa APC — Hadimin Tinubu

Ana ci gaba da tafka muhawara kan makomar siyasar Peter Obi kafin babban zaɓen 2027.

Peter Obi ya kusa dawowa APC — Hadimin Tinubu

Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya ce babban aminin Obi, Valentine Ozigbo, ya koma jam’iyyar APC domin yin takarar gwamna.

“Kun san muna rage ƙarfin jam’iyyar LP kuwa?” in ji Bwala.

“Valentine Ozigbo ya shigo jam’iyyarmu, Balami ma haka, Peter Obi ma zai zo. Idan har Ozigbo ya shigo jam’iyyar – wanda ke da kusanci da Obi – to na tabbata Obi ma zai biyo bayansa.”

Sai dai Obi bai mayar da martani kan wannan iƙirari ba.

A baya, ya sha musanta jita-jitar cewa zai bar jam’iyyar Labour Party.

Kakakin jam’iyyar, Obiora Ifoh, ya yi watsi da wannan magana, inda ya bayyana cewar wasu ’yan siyasa ne ke ƙoƙarin lalata jam’iyyar.

“Abin mamaki ne ganin yadda wasu ke ƙoƙarin haddasa matsala tsakanin jam’iyyar da shugabanninta,” in ji Ifoh.

“Peter Obi ya sha nanata cewa zai yi Labour Party cikakkiyar biyayya saboda manufofinta a kan al’umma sun dace da burinsa. Ba zai taɓa komawa wata jam’iyyar da ke kare muradun attajirai ba.”

Wasu masana siyasa na ganin cewa Obi ba zai bar Labour Party ba, domin ya samu karɓuwa sosai tun bayan zaɓen 2023.

Wasu kuwa na ganin rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar na iya tilasta masa neman wata mafaka.

Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, makomar Obi a siyasa na ci gaba da zama abin tattaunawa.

Ko zai ci gaba da kasancewa a Labour Party ko kuma zai yanke shawarar komawa wata jam’iyya, wannan mataki nasa zai taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.