Petr Cech ya koma Arsenal

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun tabbatar golan Chelsea Petr Cech ya koma kulob din Arsenal a kan Fam miliyan 10.9 kwatankwacin Naira biliyan 33 da milyan 27. Da ma an jima ana tattaunawa a tsakanin kulob din Arsenal da golan akan yiwuwarsa ta komawa kulob din, kuma ya zuwa shekaranjiya Laraba ne suka […]

Petr Cech ya koma Arsenal
Petr Cech ya koma Arsenal

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun tabbatar golan Chelsea Petr Cech ya koma kulob din Arsenal a kan Fam miliyan 10.9 kwatankwacin Naira biliyan 33 da milyan 27.

Da ma an jima ana tattaunawa a tsakanin kulob din Arsenal da golan akan yiwuwarsa ta komawa kulob din, kuma ya zuwa shekaranjiya Laraba ne suka cimma matsaya.
Jaridar Guardian ta Ingila ta kalato kulob din Arsenal ya amince ya rika biyan sabon golan albashin Fam dubu 100 kwatankwacin Naira miliyan 30 da dubu 300 a mako.
Tuni Petr Cech ya godewa mai kulob din Chelsea attajiri Roman Abramobich a kan amincewar da ya yi masa na canza sheka zuwa Arsenal duk da yake bai bar birnin Landan ba kuma yana da sauran shekara guda a kwantaraginsa da kulob din.
dan kimanin shekara 33, Petr Cech ya shafe lokaci mai tsawo yana cin benchi a kakar wasan da ta wuce tun bayan da Chelsea ta sayo golan Atletico Madrid na Sifen Thaubat Courtious al’amarin da ya tilasta shi canza sheka zuwa wani kulob.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram