Platini zai tsaya takarar shugaban Hukumar FIFA

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Mista Michel Platini ya yanke shawarar tsaya wa a zaben shugabancin hukumar FIFA da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairun 2016. Shugaban ya ce ya yanke shawarar tsaya wa takarar ce bayan wasu daga cikin shugabannin hukumomin kwallon […]

Platini zai tsaya takarar shugaban Hukumar FIFA
Platini zai tsaya takarar shugaban Hukumar FIFA

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Mista Michel Platini ya yanke shawarar tsaya wa a zaben shugabancin hukumar FIFA da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairun 2016.

Shugaban ya ce ya yanke shawarar tsaya wa takarar ce bayan wasu daga cikin shugabannin hukumomin kwallon kafa na sassan duniya sun matsa masa a kan yin haka.
Platini, wanda aka shaide shi da caccakar shugaban hukumar mai barin gado Mista Sepp Blatter, ya ce ya yanke shawarar tsaya wa takarar ce don ganin ya kawo karshen dambarwar cin hanci da rashawa da ta sarke hukumar, al’amarin da ya sa Blatter ya sauka daga kujerar jim kadan bayan an sake zabarsa a karo na biyar.
Michel Platini shi ne shugaban hukumar UEFA tun cikin shekarar 2007 watau kimanin shekaru takwas da suka gabata. Ya ce da kyar aka shawo kansa har ya amince ya tsaya takara a zaben da zai gudana a hukumar ta FIFA a watan Fabrairun badi.
Idan za a tuna Blatter dai ya sauka daga kan mukaminsa ne bayan jami’an tsaron Amurka sun yi awon gaba da 14 daga cikin jiga-jigan hukumar a kan zargin yin almundahana da hakan ta janyo aka rika yi wa shugabannin hukumar ta FIFA tofin Allah-tsine daga ko’ina a fadin duniya.
Masanar harkar kwallo suna ganin da wuya idan Michel Platini bai lashe zaben ba, don daga cikin ’yan takarar da za su fafata babu wanda ya kama kafarsa a wajen gogewa da kuma kwarewar yin shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja