Poland ta roƙi Nijeriya ta saki ’yan ƙasarta da suka ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zanga

Wisniewski ya ce bai yarda daliban sun ɗaga tutocin kasar Rasha ba.

Poland ta roƙi Nijeriya ta saki ’yan ƙasarta da suka ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zanga

Tutar Rasha

Gwamnatin ƙasar Poland ta roƙi Nijeriya da ta saki ’yan ƙasarta da aka kama suna ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a ƙasar.

Jami’an diflomasiyyar Poland a ranar Juma’a sun yi kira da a saki ’yan kasar bakwai da ake tsare da su a Nijeriya.

Rahotanni a bayan nan sun bayyana cewa an tsare wasu dalibai shida ’yan kasar Poland da wani malami daga Jami’ar Warsaw, wadanda ke halartar wani shiri na nazarin harshen Hausa a Jihar Kano.

Wani mai magana da yawun Hukumar Leƙen Asirin Nijeriya ya ce an kama su ne da laifin ɗaga tutocin ƙasar Rasha yayin zanga-zangar, abin da jami’an ƙasar Poland suka ce ba zai yiwu ba.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Poland, Jakub Wisniewski ya roƙi Nijeriya da ta ƙyale daliban da malamin su koma gida ga iyalansu, inda ya yi wa manema labarai ƙarin haske kan ƙoƙarin da kasar Poland ke yi kan lamarin bayan ganawa da mai kula da harkokin Nijeriya a Warsaw.

‘Jahiltar al’adu’

“A yayin taron, na bayyana cewa na gamsu da cewa halayen daliban na iya haifar da rashin sanin al’adu da dokokin yankin. Na roƙi yiwuwar mayar da su Poland, zuwa gidajensu, inda iyalansu ke jiransu, ”in ji Wisniewski.

Wisniewski ya ce bai yarda daliban sun ɗaga tutocin kasar Rasha ba kamar yadda TRT ya ruwaito.

Wisniewski ya ce an kai ’yan ƙasar ta Poland bakwai zuwa babban birnin tarayya Abuja, kuma suna cikin koshin lafiya, inda a jiya Juma’a aka shirya jakadan Poland zai gana da su.

Haramta zanga-zanga

Wisniewski ya yi nuni da cewa, a halin yanzu akwai dokar hana fita da kuma haramta zanga-zanga a Nijeriya, inda ake gudanar da gagarumar zanga-zanga a cikin al’ummar kasar miliyan 220 sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da yunwa.

An ga wasu ’yan Nijeriya masu zanga-zanga suna daga tutocin kasar Rasha a jihohin Arewacin kasar, suna ci gaba da yin wani irin yanayi da ake gani a Afirka a kasashen da aka yi juyin mulki, inda masu ra’ayin Rasha ke kara ta’azzara yayin da gwamnatocin soja suka yanke alaƙa da kasashen Yamma.