Priyanka ga Jarumai masu tasowa: Sai an sha wuya, akan sha dadi

Fitacciyar jarumar fina-finan Indiya Priyanka Chopra ta ba jaruman indiya masu tasowa shawara cewa sai an sha wuya akan sha dadi, sannan su bi komai a hankali idan ba sa so su yi tashin dan jaki.Ta ce hakan ne a lokacin da ta ziyarci birnin Pink City don ta yi tallar sabon fim dinta mai […]

Priyanka ga Jarumai masu tasowa: Sai an sha wuya, akan sha dadi
Priyanka ga Jarumai masu tasowa: Sai an sha wuya, akan sha dadi

Fitacciyar jarumar fina-finan Indiya Priyanka Chopra ta ba jaruman indiya masu tasowa shawara cewa sai an sha wuya akan sha dadi, sannan su bi komai a hankali idan ba sa so su yi tashin dan jaki.
Ta ce hakan ne a lokacin da ta ziyarci birnin Pink City don ta yi tallar sabon fim dinta mai suna ‘Mary Kom’. An yi fim din ‘Mary Kom’ a kan wata ’yan damben boding mai suna Mary Kom daga Manipur.
PeeCee lakabin da ake kiran jarumar, ta ce ta ji dadin abincin gargajiya na Rajasthani, wanda ya sanya ta santi da sude hannu, “Ina kaunar Pink City da kuma abincin da na ci a nan, ba na gajiya da cin gatte ki sabjee, baya ga haka ina son al’adun wannan wuri.”
Ta ce fim din ‘Mary Kom’ zai taimaka wa matasa don su ga bayan dukkan kalubale da yake ci musu tuwo a kwarya,
 “Mary Kom labari ne a kan wata mata wanda ta sha wahala a karshe ta yi dariya, Mary Kom ’yar damben boding ce, ta yi ta fadi tashi, sannan ta jajirce har ta zama gwarzuwar ’yar dambe ta duniya. Labarin na da motsa zuciya, sannan yana karfafa gwiwa.” Inji Chopra.
Daga nan ta ba jarumai masu tasowa shawarar idan har suna so tauraruwarsu ta rika haskakawa ba tare da dusashewa ba, to su bi komai a hankali ba tare da gaggawa ba.
“Shawarata ga jarumai masu tasowa ita ce, kada su rika daukar komai na rayuwa a matsayin ko-a-mutu-ko-a-yi-rai, duniya tana tafin hannunsu, za su yi yadda suke so da ita idan suka yi komai yadda ya dace. Kada su karaya ko cire tsammani, su kasance masu kyakkyawan tsammani. Kodayaushe su rika cewa ‘nahin hota toh kuch aur karr lenge’, (idan ba mu yi wannan ba, za mu samu wani abu daban”, idan har ba su samu nasarar yin wani abu ba, to hakan ba ya nufin ba za su samu nasarar yin wani abu ba kuma. Su kwantar da hankalinsu domin sai an sha wuya akan sha dadi.”