PRP ta musanta zargin Kwankwaso ya saye fom din takara 69 na Jam’iyyar
A ranar Lahadi Shugaban Dandalin Masu Ruwa da Tsaki na Arewa maso Yamma na jam’iyyar, Abdulkaɗir Musa Guza, ya yi zargin cewa Kwankwaso ya saye dukkan fom ɗin takarar PRP domin “ƙwace” jam’iyyar tare da tsayar da mabiyansa takara a cikinta.
Jam’iyyar PRP ta musanta zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya saye fom ɗin takara 69 na jam’iyyar.
A ranar Lahadi Shugaban Dandalin Masu Ruwa da Tsaki na Arewa maso Yamma na jam’iyyar, Abdulkaɗir Musa Guza, ya yi zargin cewa Kwankwaso ya saye dukkan fom ɗin takarar PRP domin “ƙwace” jam’iyyar tare da tsayar da mabiyansa takara a cikinta.
Sai dai Sakataren PRP na jihar, Alhaji Musa Maigari, ya shaida wa manema labarai a Kano a ranar Litinin cewa an riga an cika dukkan guraben takarar jam’iyyar, kuma an kammala zaɓukan fid-da-gwani, yana mai cewa Kwankwaso ba ma ɗan jam’iyyar ba ne.
Sakataren ya ce mutumin da ya yi wannan zargi ba shi da wata alaƙa da PRP, don haka ba zai iya yin magana a madadin jam’iyyar ba.
- An kashe majinyata da ma’aikatan asibiti a harin Filato
- An kama ɗan kasuwa yana sayar da gurɓatacciyar madara a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Me ya sa mutane suka dawo daga rakiyar Kirifto?
“Mutumin da ya yi waɗannan zarge-zarge ba ma mambanmu ba ne. Abin dariya ne a wannan lokaci da aka riga aka kammala zaɓukan fid-da-gwani, wani ya fito yana magana kan zaɓukan fid-da-gwani ko sayar da fom din takara,” in ji Maigari.
Ya jaddada cewa babu wani bayani ko rajistar wata mu’amala tsakanin Kwankwaso ko wakilansa da sakatariyar jam’iyyar.
Maigari ya ƙara da cewa lokacin da aka yi wannan zargi bai dace ba, domin kuwa PRP ta riga ta kammala zaɓukan fid-da-gwani domin tunkarar zaɓe mai zuwa.
Sakataren jam’iyyar ya buƙaci al’umma su yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin “jita-jita marasa tushe”, tare da jaddada cewa su dogara ne kawai da bayanan da ake fitarwa ta hanyoyin hukuma na jam’iyyar.