PRP ta yi fatali da shirin kafa ’yan sandan jihohi
Jam’iyyar ta bayyana cewa, shirin kafa ’yan sandan jihohi a wannan lokaci na haifar da shakku, saboda haka bai kamata a aiwatar da shi ba.
Jam’iyyar PRP ta bayyana adawarta ga shirin kafa ’yan sandan jihohi, tana mai cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da ƙwarin gwiwa da amincewar jama’a da za ta aiwatar da irin wannan babban sauyi.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed ya fitar, PRP ta ce duk da cewa Najeriya na buƙatar gyaran tsarin tsaro, gwamnatin a yanzu ta gaza tafiyar da hukumomin tsaron da ake da su.
- Sojoji sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa a Zamfara
- An umarci bankuna su rufe asusun masu alaƙa da ta’addanci
Jam’iyyar ta bayyana cewa, shirin kafa ’yan sandan jihohi a wannan lokaci na haifar da shakku, saboda haka bai kamata a aiwatar da shi ba.
PRP ta buƙaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen magance matsalar rashin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, maimakon ƙoƙarin sauya tsarin aikin ’yan sanda.
Har ila yau, jam’iyyar ta ce ya kamata a dakatar da batun kafa ’yan sandan jihohi har sai bayan babban zaɓen 2027.