PSG ta dauki Golan AC Milan, Gianluigi Donnarumma

Donnarumma ya rattaba hannu kan kwantaragin shekara biyar.

PSG ta dauki Golan AC Milan, Gianluigi Donnarumma

Gianluigi Donnarumma

Paris Saint-Germain ta tabbatar da sayen Golan AC Milan, Gianluigi Donnarumma, kwanaki bayan ya taimaka wa Italiya ta lashe gasar Euro 2020.

A watan Yuni ne Donnarumma ya bar AC Milan, bayan kwantaraginsa ya kare da kungiyar mai buga gasar Serie A.

Dan wasan mai shekara 22, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da za ta dauke shi zama a PSG har zuwa watan Yunin shekarar 2026.

Tun a Larabar da ta gabata ce Donnarumma ya rubuta wata budaddiyar wasiki zuwa ga magoya bayan AC Milan, kwana guda gabanin komarwasa PSG.

A lokacin da yake shekara 16 kacal, Donnarumma ya samu shiga babbar tawagar AC Milan bayan an dauko shi daga tawagar Matasa ta kungiyar a shekarar 2015.

Tun daga wannan lokaci likafarsa ta daga, inda ya zama mai tsaron raga zabin farko, kuma ya ci gaba da zama a matsayin har zuwa lokacin da ya bayar kungiyar a bana.