PSG za ta yi wasa da Bayern Munich ba Mbappe
Mbappe ba zai buga wasannin lig da za su kara da Touluse, Monaco da Lille ba.
Da alama Kylian Mbappe ba zai buga wasan da Paris Saint-Germain za ta yi da Bayern Munich a wasan zagayen farko na ‘yan 16 a Gasar Zakarun Turai ta Champions League saboda raunin da ya ji a kafarsa.
Dan wasan gaban mai shekaru 24 da haihuwa ya ji rauni a farkon rabin lokaci a wasan da PSG ta doke Montpellier da ci 3-1 a ranar Laraba da ta gabata, kuma zai yi jinyar kusan makonni uku.
- Gobe ake muhawarar ’yan takarar Gwamnan Kano
- Kokowar Ganduje, Kwankwaso da Shekarau wajen kwace Kano
Zakarun na Faransa sun fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis, inda suka bayyana kiyasin lokacin da Mbappe zai warke.
A sanarwar da PSG ta fitar wadda idan har lamarin ya tabbata, ba zai buga wasannin lig da za su kara da Touluse, Monaco da Lille ba, da wasan Coupe de France da Marseille, da kuma wasansu na farko a gasar Zakarun Turai a gida da Bayern, wanda za a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu.
“Bayan gwaje-gwaje, Kylian Mbappe ya samu rauni a cinyarsa ta hagu. An kiyasta lokacin da zai dawo zuwa makonnin uku,” in ji kungiyar PSG.
Mbappe, wanda ya zura kwallaye 25 a wasanni 26 da ya buga wa PSG a kakar wasa ta bana, ya yi wasan da ba zai manta ba a ranar Laraba, yayin da mai tsaron raga ya buge fenaratin da ya buga, ciki har da wadda ya sake bugawa ta yi sama, sannan aka cire saboda rauni a minti na 21 da fara wasa.
Kulob din ya kuma tabbatar da cewa za’a yi wa Sergio Ramos gwaje-gwaje, bayan da tsohon dan bayan Sifaniya shi ma aka cire shi a karawar da suka yi da Montpellier bayan da ya ji rauni a kai.