Putin ya lashe zaben Rasha karo na biyar
Putin ya samu nasarar lashe kashi 87 cikin dari na kuri’un da aka kada.
Vladimir Putin ya sake lashe zaben Rasha karo na biyar a wani sabon wa’adi na zama a karagar mulki kamar yadda sakamakon zaben ya nuna a ranar Lahadi.
Putin mai shekaru 71 ya samu karin waadin mulki na tsawon shekaru 6 wanda tsohon jami’in leken asirin zai kasance wanda ya fi dadewa a kan karagar mulkin Rasha a cikin shekaru 200.
- Yadda Za Ku Samu Sadarwa Da Intanet A Lokacin Da Aka Samu Tangarɗa
- Ban taba karbar albashi ba tun da na hau mulki — Soludo
Sakamakon da aka tattara a yayin da masu zabe ke barín rumfunan kada kuri’a ya nuna cewa Putin ya samu nasarar lashe kashi 87 cikin dari na kuri’un da aka kada bayan da aka rufe rumfunan zabe a yankin Kaliningrad na yammacin kasar.
Fadar Kremlin ta bayyana zaben a matsayin wata dama da al’ummar kasar za su yi amfani da ita wajen bayyana goyon bayansu ga matakin sojin da take dauka a kan Ukraine, inda ma har aka kada kuri’a a yankunan Ukraine da ke karkashin ikon Rasha.
A jawabin da ya gabatar a wani taron manema labarai a wannan Litinin, bayan wannan sakamako, Putin ya ce Rasha ba za ta mika wuya ga duk wata barazana ba, a yayin da yake jinjina wa al’ummar kasar da suka ba shi karin wa’adi musamman ma dakarun Rasha da ke fagen daga a Ukraine.
A waje daya kuma, Ukraine da kawayenta sun caccaki wannan sakamako, su na mai bayyana zaben a matsayin na jeka-na-yi-ka, a yayin da shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana Putin a matsayin dan kama-karya, wanda giyar mulki ke tasiri a kansa.
Amurka ta ce kwata-kwata babu batun sahihanci ko adalci a zaɓen, tare da tunasar da cewa Putin ya garkame abokan hamayyarsa na siyasa, da kuma datse sauran daga shiga takara.
Haka ita ma Poland ta yi irin wadannan zarge-zarge na tauye yancin dimokuradiya.
Sai dai shugaban Venezule, Nicolas Maduro, ya yi murna da nasarar Vladimir Putin.
Ya ce tabbas Putin ya yi nasara a yaƙinsa shi ɗaya tilo da illahirin ƙasashen yamma da suka haɗe masa kai.
“Wannan na sake fito da martaba da akidun al’ummar Rasha wanda hakan ya kai ga wannan nasara ta Shugaba Vladimir Putin.
“Wannan nasara na sake buɗe sabon babin rayuwa a Rasha a wannan duniya na taron dangi. Don haka dan uwanmu, Vladimir Putin ya basu kunya da nasararsa.”
Idan Putin ya kammala wannan wa’adi, zai kasance shugaban Rasha mafi dadewa a kan karagar mulki tun bayan Catherine the Great a karni na 18.