Qananan bankuna na bunqasa kasuwanci – Yakasai
An bayyana cewa bankunan ba da rance ga masu qananan sana’o’i watau “ Microfinance Banks” sun qara bunqasa harkokin kasuwanci da kyautata yanayin qananan sana’o’i a fadin jihar kano musamman a wannan lokaci da ake ci da ake ciki. Wannan bayani ya fito ne daga mataimakin manajan bankin ba da rance ga masu qananan sana’o’i […]

An bayyana cewa bankunan ba da rance ga masu qananan sana’o’i watau “ Microfinance Banks” sun qara bunqasa harkokin kasuwanci da kyautata yanayin qananan sana’o’i a fadin jihar kano musamman a wannan lokaci da ake ci da ake ciki.
Wannan bayani ya fito ne daga mataimakin manajan bankin ba da rance ga masu qananan sana’o’i na Bichi Alhaji Rabi’u Yahaya Yakasai a ganawarsa da wakilinmu, inda kuma ya sanar da cewa yanzu al’umma sun fahimci manufar kafa wadannan bankuna, sannan masu sana’o’i qanana da matsaqaita suna amfani da bankunan wajen bunqasa harkokinsu na kasuwanci ba tare da wata fargaba ba.
Haka kuma ya nunar da cewa gwamnatin jihar kano tayi tunani mai kyau wajen ganin kowace qaramar hukuma tana da a qalla banki daya wanda hakan ta sanya al’uma dake yankunan karkara suke yin hulda kai tsaye da cibiyoyin kudi domin bunqasa harkokin su na kasuwanci batare da wata matsala ba.
Alhaji Rabi:u Yakasai ya bada misali da yadda bankin bada rance ga masu qananan sana’oi na Bichi ya bada fiye da naira miliyan arba’in da shida ga al’umar wannan yanki domin su fadada sana’o in su wanda a cewar sa haka ya qara zaburar da masu sana’oi wajen ruvanya harkokin su na cinikayya cikin sauqi.
Dangane da bankin yake tafiyar da aiyukan sa kuwa, jami’in ya bayyana cewa daga kafa wannan banki zuwa yanzu, an sami ingantuwar kasuwanci da cinikayya batare da samun wata matsala ba, inda kuma ya sanar da cewa bankunan bada rance ga masu qananan sana’oi suna aiki ne domin ganin an bunqasa tattalin arziqin al’uma da masu qanana sana’oi kamar yadda ake gani a yanzu.
Sannan yayi amfan da wannan dama wajen yin godiya ga al’umar qaramar hukumar Bichi da kewaye saboda yadda suka fahinci manufofin kafa wadannan bankuna na bada rance ga masu qananan sana’oi tareda godiya ga manajan bankin Alhaji Shehu Bappa Usman da dukanin ma’aikatan bankin bisa qoqarin da ake yi wajen tallafawa al’uma don bunqasa tattalin arziqi da kasuwanci.
A qarshe Alhaji Rabi’u Yahaya Yakasai ya buqaci al’uma masu qananan sana’oi da masu qananan masana’antu da kuma qungiyoyi dake harkokin kasuwanci dasu riqa hulda da bankunan bada rance ta yadda zasu sami qarin damar bunqasa kasuwancin su batare da jinkiri ba, sannan ya shawarci gwamnatin jihar kano da ta vulo da qarin hanyoyi na qarfafa wadannan bankuna musamman ganin cewa suna da amfani ga al’uma kwarai da gaake.