Qarancin jari ne matsalata – Musa Tela
Wani fitaccen Tela mai suna Musa Labaran ya ce qarancin jari shi ne babban qalubalen da yake fuskanta a sana’arsa ta dinki. Musa wanda ya fi qwarewa a fannin yi wa yadi qwalliya wato (Designing) ya yi furucin ne yayin da yake tattauna wa da Aminiya, a qarshen makon da ya gabata. “Kasan kowane […]
Wani fitaccen Tela mai suna Musa Labaran ya ce qarancin jari shi ne babban qalubalen da yake fuskanta a sana’arsa ta dinki.
Musa wanda ya fi qwarewa a fannin yi wa yadi qwalliya wato (Designing) ya yi furucin ne yayin da yake tattauna wa da Aminiya, a qarshen makon da ya gabata.
“Kasan kowane dan adam ba ya rasa ’yan matsalolin da yake fuskanta. Ni gaskiya babban qalubalen da nake fuskanta shi ne qarancin jari”. Inji
Musa wanda shi ne shugaban kamfanin “Sa’a Teloring” ya bayyana cewa idan da yana da jari mai qarfi da ya fadada sana’arsa har ya dauki qarin yara masu yawa.
Ya bayyana cewa ya yi kimanin shekaru 28 yana gudanar da sana’ar dinki a garuruwa dadaban-daban da suka hada da Zariya da Sakkwato da kuma Jihar Kano.
Ya ci gaba da cewa ya shiga sana’ar da qafar dama domin ya samu nasarori da ya yawa wadanda suka hada da yin aure da koyawa yara da yawa wadanda a yanzu suke zaman kansu.
Ya bayyana cewa ya tashi ya ga yayyensa suna yin sana’ar a gidansu saboda haka sai shi ma ya shiga don ya koyi sana’ar.
Ya qara da cewa cikin shekara guda ya koyi sana’ar a garin Zariya da ke cikin jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa ya qware sosai a fanin aikin sama da na qasa na maza da na mata.
Telan dan kimanin shekaru 38 a duniya ya bayyana cewa batun rashin cika alqawari da ake zargin teloli da shi batu ne wanda rashin haquri ke janyo shi.
Ya bayyana cewa idan da teloli za su rage hadama su kuma abokanen huldarsu za su riqa yin haquri da ba za tava samun matsala ba.
Ya shawarci masu sana’ar dinki su riqa yin gaskiya kuma su riqe amanar da jama’a suka ba su.
Ya bayyana cewa haquri da riqon amana shi ne sirrin nasarorin day a samu a sana’arsa ta dinki.
Ya ce burinsa shi ne ya taimakawa yaransa su ma su tsaya da qafarsu ta yadda za su taimakawa al’umma.