Qatar 2022: Abubuwan da suka faru bayan bai wa Qatar daukar nauyin gasar Kofin Duniya
Daga lokacin yanzu, an yi shekara 12 ana ce-ce-ku-ce da nuna yatsa, shi ya sa Aminiya ta kalato wasu muhimman abubuwa da suka faru.
A shekarar 2010 ce aka sanar da kasar Qatar a matsayin wadda za ta dauki nauyin gasar ta bana.
Daga lokacin yanzu, an yi shekara 12 ana ce-ce-ku-ce da nuna yatsa. Hakan ya sa Aminiya ta kalato wasu muhimman abubuwa da suka faru.
- Qatar 2022: Zargin tauye hakkokin baki ya dabaibaye Qatar
- Qatar 2022: Rikita-rikitar da aka yi kafin amincewa da Gasar Kofin Duniya a Qatar
2 ga Disamba, 2010
Ranar da aka sanar da Qatar a matsayin kasar da za ta dauki nauyin gasar, inda ta zamo da farko a yankin Larabawa.
5 ga Mayu, 2011
Ranar da aka dakatar da Mataimakin Shugaban Hukumar FIFA na lokacin, Jack Warner bayan an samu sakon imel na Janar Sakataren FIFA na wancan lokacin, inda ya yi zargin cewa Qatar ta sayi dammar daukar nauyin gasar ne da kudinta.
10 ga Mayu, 2011
Aka samu bayani daga jaridar Sunday Times cewa Shugaban Hukumar Kwallon Afirka na wancan lokacin, Issa Hayatou na kasar Kamaru da Jacques Anouma na Ivory Coast sun karbi rashawa domin zabar Qatar, wanda hakan ya sa aka dakatar da su biyun tare da Amos Adamu na Najeriya, duk da cewa sun karyata zargin.
17 ga Yuli, 2012
Shugaban FIFA na wancan lokacin, Sepp Blatter ya sanar da cewa Tsohon Atoni-Janar na Amurka, Michael Garcia da wani alkali daga Jamur, Hans-Joachim Eckert za su gudanar da bincike kan lamarin.
17 ga Mayu, 2014
Wani rahoto ya bankado yadda Warner ya karbi cin hancin Dala miliyan 2 daga Qatar.
13 ga Nuwamba, 2014
Aka fitar da sakamakon binciken kwamitin FIFA, inda a ciki aka wanke Qatar daga aikata ba daidai ba.
24 ga Fabrairu, 2015
Aka mayar da Gasar Kofin Duniya watan Nuwamba saboda yanayin zafin Qatar.
25 ga Satumba, 2015
FIFA ta sanar da za a fara Gasar Kofin Duniya a ranar 21 ga Nuwamba.
29 ga Satumba, 2015
FIFA ta dakatar da Warner daga harkokin kwallon kafa na har abada saboda samun sa da laifin cin hanci.
19 Mayu, 2017
Aka kammala Filin Wasa na Khalifa International Stadium a matsayin fili na farko da ya shirya domin gasar.
16 ga Mayu, 2019
Aka kammala Flin Wasa na Al Janoub, wanda shi ne na farko da aka gina musamman domin gasar.
18 ga Yuni, 2019
’Yan sanda a Faransa suka kama tsohon Shugaban UEFA, Michael Platini bisa zargin karbar rashawa domin bayar da dammar daukar nauyin gasar ta bana. Amma aka sake shi daga baya.
8 ga Disamba, 2020
Qatar ta amince da ka’idojin FIFA na mutunta bambancin yanayin mutane, musamman bayan batun shan giya da batun masu luwadi da ’yan madigo ya taso.
19 ga Janairu, 2022
Aka fara sayar da tikitin zuwa kallon gasar a Qatar daga farashin mazauna kasar na Riyal 40, wato Dala 11, wanda shi ne mafi sauki tun bayan farashin tikitin gasar na Mexico na 1986.
8 ga Yuni, 2022
Kotu a Sweizerland ta wanke Sepp Blatter da Platini daga aikata ba daidai ba.
11 ga Agusta, 2022
FIFA ta sanar da rage kwana daya a ranar fara gasar, aka mayar da wasan farko ranar 20 na Nuwamba, maimakon ranar 21.