Qatar 2022: Argentina ta kai Kwata-Fainal
Messi ne ya ci kwallo na farko a wasan da Argentina ta casa Austaraliya 2-1 a Matakin ’Yan 16 na Gasar Kofin Duniya
Kasar Argentina ta casa Austaraliya da 2-1 a wasan Matakin ’Yan 16 na Gasar Kofin Duniya.
Da haka Argentina ta zama kasa ta biyu da ta tsallaka zuwa Kwata-Fainal, bayan Netherlands da ta casa Amurka da 3-1 a gasar da ke gudana a kasar Qatar.
A minti na 35 ne babban dan wasan Argentina, Lionel Messi, ya zura kwallonsa na farko a matakin a ragar Australiya.
Daga bisani Julian Alvarez ya kara wa Australiya, kafin cikar awa daya da fara wasan.
Ana sa ran kasashen biyu da suka fara haura Matakin ’Yan 16 — Argentina da Netherlands — za su kara da juna a matakin na Kwata-Fainal.
Tuni dai aka tisa keyar kasashe 16 zuwa gida bayan da suka zama tayar baya a Matakin Rukuni na Gasar Kofin Duniya ta farko a Yankin Gabas ta Tsakiya.
Kasashen da suka zo na daya da na biyu a kowane rukuni ne suka tsallaka zuwa mataki na biyu — ’Yan 16.
Sauran wasannin da aka fafata a ranar Asabar su ne tsakanin Faransa da Poland; Birtaniya da Senegal; Japan da Croatia; Brazil da Koriya Ta Kudu; Moroko da Spain; sai kuma Portugal da Switzerland.