Qatar 2022: Argentina ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya ta bana

Kana na nufin burin Kyaftin din tawagar kasar, Lionel Messi ya cika

Qatar 2022: Argentina ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya ta bana

Kasar Argentina ta lashe Kofin Duniyar da aka gudanar a kasar Qatar, bayan ta doke mai rike da kofin, wato kasar Faransa a bugun fanareti.

Argentina dai ta samu nasarar ce da yammacin Lahadi, bayan da ta zira kwallo hudu ragar Faransa, wacce ita kuma ta zira mata biyu a bugun na fanareti.

Wannan dai shi ne karo na uku da Argentina take lashe kofin mafi kololuwar daraja a duniyar kwallon kafa.

Nasarar ta Argentina dai ta sa burin Kyaftin din tawagar kasar, kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG, Lionel Messi, na daga wa kasarsa kofin, ya cika.

Messin me dai ya fara zura wa Argentina kwallo a raga a minti na 23 da fara wasan, sai Angel Di Maria ya kara ta biyu a minti na 36.

To sai dai bayan dawowa hutun rabin lokaci, dan wasan Faransa, Kylian Mbappe, ya farke wa kasarsa kwallo ta hanyar ci mata guda biyu, kuma haka aka ci gaba da fafata wasan har aka tashi.

Daga nan ne aka je karin lokaci, amma duk da haka ba a sami wanda ya yi nasara ba, sai da aka kai ga bugun fanaretin.

Kyaftin din Argentina, Messi yana daga kofin
Kyaftin din Argentina, Messi yana daga kofin

A baya, kasar ta Argentina ta taba lashe kofin sau biyu a shekarun 1978 da 1986.

Kazalika, kasar ta zo na biyu a gasar har sau uku a shekarun 1930 da 1999 da kuma 2014.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa