Qatar 2022: Barcelona ta kafa tarihi a Gasar Cin Kofin Duniya
Yanzu haka kungiyar na da ’yan wasa 17 da ke buga gasar
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain ta kafa tarihin zama kungiyar da ta fi yawan ’yan wasan da ke buga kofin duniya a gasar da yanzu haka ake gudanarwa a Qatar.
Yanzu haka dai kungiyar na da ’yan wasanta har guda 17, adadin da ya haura guda 15 din da suka buga wasa daga kungiyar ga kasar Brazil a shekarar 2014.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Bauchi Da Gombe Ke Kallon Hakar Mai A Yankinsu
- Yau ake fara hako danyen mai a Arewacin Najeriya
Kungiyar Bayern Munich da Manchester City ne suke biye wa Barcelona baya da yawan ’yan wasa 16, kowaccensu.
A mataki na uku kuwa, kungiyar Al-Sadd da ke kasar Qatar ce da ‘yan wasa 15, sai Manchester United ta Ingila mai ’yan wasa 14 da ke buga gasar a yanzu haka.
Su kuwa kungiyoyin Real Madrid da Chelsea da Athletico Madrid da kuma Al-Hilal ta kasar Saudiyya, dukkansu na da ’yan wasa 12 da ke buga wa kasashe daban-daban gasar.
An dai fara gudanar da gasar ta bana ce a kasar Qatar ranar Lahadi, karon farko a tarihi da wata kasar Larabawa ta karbi bakuncin shirya gasar.