Qatar 2022: Birtaniya ta kora Senegal gida da ci 3-0
Moroko ce kadai kasar Afirka da ta rage kuma take neman zuwa Kwata-Fainal a gasar da ita ce ta farko a Yankin Gabas ta Tsakiya.
Kasar Senegal ta fice daga Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022 bayan tawagar ’yan wasan Birtaniya ta lallasa ta da ci 3-0.
Yanzu Birtaniya ta shiga sahun kasashen da za a fafata da su a matakin Kwata-Fainal, bayan dan wasanta, Jordan Henderson ya zura kwallon farko a minti na 38, Harry Kane ya kara a minti 48, sannan Bukayo Saka ya zura ta uku a minti 57 a ragar Senegal.
Da wannan rashin nasara a wasan na ranar Lahadi, ta tabbata Senegal ta shiga sahun kasashen Afirka, Kamaru da Ghana cikin masu dawowa gida bayan an doke su a Matakin ’Yan 16.
A daya bangaren kuma, tawagar ’yan wasan Birtaniya ta kai hari takwas a gidan Senegal, inda ta yi nasara zura uku daga cikin hudu da suka nufi ragar.
Bayan doke Senegal zuwa Kwata-Fainal, Birtaniya za ta fuskaci Faransa mai rike da kofin gasar, wadda ke kokarin kafa tarihin zama kasar da ta kare kambunta a shekara 60 da suka gabata.
A tarihin Gasar Kofin Duniya na FIFA, Italiya ce kasar da ta fara kare kambunta na 1934 a 1938, sai Brazil da ta lashe kofin a 1958 ta kuma kare shi a 1962.