Qatar 2022: Croatia ta tsallaka kwata fainal bayan ta lallasa Japan
Hakan dai na nufin ta cire Japan daga gasar ta bana
Kasar Croatia a ranar Litinin ta cire takwararta ta Japan daga Gasar Cin Kofin Duniyar da ke gudana a Qatar ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Hakan dai na nufin yanzu Croatia ta sami tsallakawa matakin kwata fainal ke nan a gasar.
- Jiragen yaki sun hallaka ‘yan ta’adda 7 da ake nema ruwa a jallo a Kaduna
- Ban taba faduwa zabe ba a rayuwata — Tinubu
Tawagar Croatia dai ta sami nasara a kan ta Japan ne da ci uku da daya.
’Yan wasan Croatia, Mario Pasalic da Ivan Perisic ne suka ci mata kwallayen a mintuna na 55, bayan dan wasan Japan, Daizen Maeda ya fara jefa musu kwallo tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Yanzu dai Croatia za ta fafata ne da kasar Brazil wacce ita ma ta sami nasara a kan Koriya ta Kudu a wasan da suka fafata da yammacin Litinin din.
Kasar Japan dai ta fuskanci yankan kauna ne a burinta na kai wa matakin na kwata fainal karon farko a tarihinsu, duk da cewa su ne suka fi kowa yawan maki a matakin rukunin da suka fito na ‘E’.
Yanzu dai duk ragowar kasashe takwas din da suka ci wasanninsu su ne za su tsallak zuwa mataki na gaba, yayin da su kuma wadanda aka lalla za su tattara komatsansu su koma kasashensu.