Qatar 2022: FIFA ta haramta sayar da giya a kusa da filayen wasa

An umarci kamfanin giya na Budweiser, babban mai daukar nauyin harkokin FIFA, da ya kawar da rumfunansa

Qatar 2022: FIFA ta haramta sayar da giya a kusa da filayen wasa

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta haramta sayar da giya a kusa da filayen wasanni a Gasar Kofin Duniya na bana.

A ranar Juma’a FIFA ta sanar da hakan, kwana biyu kacal kafin fara gasar a kasar Qatar bayan tattarawar da bangarorin biyu suka yi.

FIFA ta sanar a ranar Juma’a cewa, “Bayan tattaunawa da hukumomin Qatar an yi ittifakin takaita sayar da giya zuwa wurare da bukukuwa da aka ware wa baki da suka je kallon gasar.

“Sauran wurare kuma za a cire rumfunan sayar da giya, haka ma a zagayen filayen wasanni gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022.

“Sauran kayan sha kuma wannan bai shafe su ba, kuma za a ci gaba da sayarwa a filayen wasannin gasar.”

Hakan na zuwa ne bayan FIFA ta sanar cewa hukumomin Qatar sun takaita shan giya da dangogin sa ga sansanoni da otel-otel da aka ware wa baki da suka je kasar kallon gasar.

Tuni dai aka umarci kamfanin giya na Budweiser, wanda shi ne babban mai daukar nauyin harkokin FIFA, da ya kawar da rumfunansa daga fitattun wurare.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos