Qatar 2022: Luis Enrique ya ajiye aikin horar da Sifaniya
Kocin ya dora alhakin rashin nasarar tawagar a kansa.
Kocin tawagar ’yan wasan Kasar Sifaniya, Luis Enrique, ya ajiye aikinsa, sa’o’i 48 bayan rashin nasara a hannun kasar Maroko a Gasar Kofin Duniya.
Sifaniya dai ta yi rashin nasara ne a bugun fanareti a rukunin ’Yan 16, inda babu dan wasanta daya da zura kwallo a raga.
- Takaita cire kudi: Majalisa za ta yi zama kan dokar CBN
- Sabbin dokoki 6 da CBN ya fitar kan takaita yawon tsabar kudi
Magoya bayan Sifaniya sun dora laifin rashin nasarar a kan kocin, tare da zargin sa da nuna son rai wajen zabar ’yan wasan da suka doka wa kasar wasa a Gasar Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar.
Luis Enrique ya ki daukar kyaftin din tawagar, Sergio Ramos daga PSG, Tiago Alcantra daga Liverpool, Gerrard Merono daga Villarreal, David De Gea daga Manchester United da sauran zaratan ’yan wasa.
Wasu masu sharhi kan harkar kwallon kafa na ganin kocin ya fifita ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ya taba horarwa a baya.
Kocin dai ya zabi ’yan wasan Barcelona takwas wadanda suka hada da; Jordi Alba, Sergio Busquet, Alex Balde, Pedri, Gavi, Eric Garcia da Ansu Fati.