Qatar 2022: Maroko ta lallasa Portugal a Gasar Cin Kofin Duniya

Hakan ya sa sun zama ƙasar Afirka ta farko da ta kai matakin

Qatar 2022: Maroko ta lallasa Portugal a Gasar Cin Kofin Duniya

Kasar Maroko ta kafa tarihin zama kasar Afirka ta farko a da ta kai matakin wasan dab da na karshe a Gasar Cin Kofin Duniya da yake gudana a kasar Qatar.

Kasar dai ta sami nasarar ce bayan ta doke tawagar Portugal da ci daya mai ban haushi a wasan dab da na kusa da na kashe a ranar Asabar.

Dan wasan kasar, Youssef En-Nesryri ne ya jefa kwallo a ragar Portugal ana minti na 42 da fara wasan, haka kuma kungiyar ta ci gaba da tsare gidanta har aka tashi wasan.

Ko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai da alkalin wasa ya ba dan wasan Maroko, Walid, Cheddiira, jan kati, amma duk da haka ba gwiwoyinsu ba su yi sanyi ba.

A baya dai, Maroko ta kafa wani tarihin bayan ta lallasa kasar Spain a zagayen rukunin ‘yan 16, sabani hasashen da aka sha yi cewa ba za ta kai labari ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos