Qatar 2022: Sabbin Abubuwa 8 A Gasar Kofin Duniya
Karon farko a Gabas ta Tsakiya, mata za su fara alkalanci, za a yi amfani da na’urar gano satar gida, an kara yawan sauyin ’yan wasa da tawagar kasashe
Kwanaki biyar suka rage a soma gasar kwallon kafa ta cin Kofin Duniya a kasar Qatar, bayan shekara hudu da yin irinsa a kasar Rasha a 2018.
Ga jerin wasu abubuwa sabbi da za a gani a gasar ta bana, wadda kasashe 32 za su fafata a gaban ’yan kallo kimanin 1.2 a Doha, babban birnin kasar Qatar.
- La’eeb: Abin da dan aljanin Gasar Kofin Duniya na Qatar ke nufi
- Kasaitattun wasanni 5 kafin Gasar Kofin Duniya na 2022
1. Karon Farko A Gabas Ta Tsakiya: Wannan shi ne karon farko a tarihi da wata kasar Larabawa da ma daukacin yankin Gabas ta Tsakiya ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya.
2. Alkalan wasa mata: A karon farko mata za su yi alkalancin wasa a tarihin gasar. An nada mata uku a cikin mutum 36 da za su yi alkalancin wasannin — Matan su ne Stephanie Frappat daga kasar Faransa da Yoshimi Yamashita daga Japan sai Salima Mukansanga daga Ruwanda. Akwai kuma karin mata 69 da za su je gasar a matsayin mataimakan alkalan wasa.
3. Na farko a watan Nuwamba: Qatar 2022 shi ne gasar Kofin Duniya na farko da za a buga watan Nuwamba zuwa Disamba, sabanin na shekarun baya da aka saba yi a watan Yuni zuwa Yuli. An sauya lokacin ne domin guje wa yanayin zafin Qatar da kan kai maki 50 a ma’aunin selshos a Yuni-Yuli, zuwa Nuwamba/Disamba inda yanayin zafin ke komawa tsakanin maki 14 zuwa 31 na ma’aunin selshos.
4. Karin sauyin ’yan wasa: A karon farko kowace tawaga za ta iya yin sauyin ’yan wasa biyar a wasa guda, sabanin uku da aka saba yi a baya. Idan wasa ya shiga karin lokaci, an yarje wa kowane bangare yin sauyin dan wasa guda daya.
5. Karin ’yan wasa: An sahale wa kowacce tawaga tura ’yan wasa 26, wato karin mutum uku kan na gasar da aka yi a Rasha. Haka ma an kara yawan ’yan wasan da za su gabatar na sharar fage daga 35 zuwa 55.
6. Na’urar gano satar gida: Za a fara amfani da wannan fasaha ta zamani da za ta gano, ta dauki hoton dan wasan da ya yi ta kuma bayyana domin ’yan kallo, har a gidajensu su gane dalilin da alkalin wasa ya yanke hukunci.
2. Tsukakken wurin gasa: Za a yi gasar ne a kasar mafi kankanta da ta taba daukar nauyin gasar ta FIFA a tarihi. Dukkkanin filayen da za yi wasannin ba su da nisa da juna a birnin Doha mai fadin kilomita 50. Wasu filayen wasan za buga wasa a cikin har sau hudu a rana kuma ana hasashen samun cinkoso sakamokon halartar mutane kimanin miliyan 1.2.
8. Mafi tsada a tarihi: Qatar 2022 ita ce gasar Kofin Duniya mafi tsada a tarihi mai masaukin baki ta kashe Dala biliyan 229 a kai. Adadin kudin ya fi ninki hudu na jimillar kudin da aka kashe wa gasar a tsawon shekara 32 da suka gabata daga 1990. Jimillar kudaden da aka kashe ka gasanni 8 da aka yi a tsawon shekarun Dala biliyan 48.63 ne.
Al Jazeera