Qatar 2022: Yau za a fara Gasar Cin Kofin Duniya
Aminiya za ta kawo muku rahotanni na musamman da wainar da ake toyawa gasar ta farko a yankin Larabawa.
A yau Lahadi, 20 ga Nuwamba ne za a fara fafata Gasar Cin Kofin Duniya na bana a kasar Qatar.
Aminiya za ta rika kawo rahotanni na musamman kan wainar da ake toyawa a gasar wadda ita ce ta farko da ake bugawa a yankin Larabawa.
Za a fafata gasar wadda ita ce karo na 22 daga 20 ga Nuwamban zuwa 18 ga Disamban bana.
- Qatar 2022: Benzema ba zai buga wasa ba… —Faransa
- Qatar 2022: FIFA ta nada Sunday Oliseh a kwamitin kwararrunta kan Kofin Duniya
Za a bude gasar ne da wasa tsakanin kasar Qatar mai masaukin baki da kasar Ecuador da misalin karfe biyu na rana.
Aminiya ta ruwaito cewa wannan ne karon farko da za a fafata gasar yankin Larabawa.
Yanayin kasar Qatar na zafi da addinin kasar ya haifar da tsaiko kan shirin karbar bakuntarta, baya ga batun cin hanci da ya dabaibaye shirin kasar na karbar bakuncin gasar.
Filayen wasan da za a buga wasannin gasar
Lusail:
Yana daukar mutum 80,000 kuma a bana aka gina shi a birnin Lusail domin gasar.
A Filin Wasan Lusai ne za a buga Wasan Karshe.
Al Bayt:
Filin Wasan Al Bayt an gina shi ne a sherakarar 2021 a birnin Al Khir, kuma yana daukar mutum 60,000 kuma a filin ne za a buga Wasan Farko.
Al Janoub:
Tun a shekarar 2019 aka bude shi a birnin Al Wakrah, kuma yana daukar mutum 40,000.
Ahmad Bin Ali:
Yana daukar mutum 40,000 kuma a shekarar 2020 aka bude shi a birnin Al Rayyan.
Khalifa International:
Tsohon filin wasa ne da aka gina tun a shekarar 1976 a Doha, babban birnin kasar kuma yana daukar mutum 40,000.
A filin ne za a buga wasan cire kasa ta uku.
Filin Wasan Education City:
Shi ma a birnin Doha yake kuma yana daukar mutum 40,000 sannan a shekarar 2020 aka bude shi.
Stadium 974:
Yana daukar mutum 40,000 kuma a bara aka gina shi a birnin Doha.
Al Thumama:
Yana daukar mutum 40,000 kuma a bara aka gina shi a Doha.
Kananan filaye: Filin Wasan Ras Abu Aboud da Filin Wasan Education City da aka gina a bara.
Tanade-tanaden Musulunci:
Kasancewar Qatar kasa ce Musulunci, ta yi wasu tanade-tanade domin kiyaye wasu dokoki na Musulunci da hana ya sa wasu malaman Musulunci suka ji dadi, yayin da a gefe guda kuma kasashen Yamma suke Allah wadai.
Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Farfesa Umar Labdo ya ce a game da gasar, “Gasar Kofin Duniya mai bambanci da sauran. Muna alfahari da kasar Qatar.”
Shehin malamin ya yi wannan batun ne a kasan wani rubutu da ya nuna cewa Qatar din ta yi tanade-tanade domin yada addinin Musulunci a daidai lokacin da ake gasar.
Daga cikin abubuwa da ta yi akwai rubuta Hadisan Manzon Allah (SAW) a alluna da cikin dakunan otel-otel a birnen da za a buga gasar.
Akwai kuma hana shan giya, duk da makudan kudaden da za ta kashe domin fansar kamfanin giyar da take cikin masu daukar nauyin gasar.
Haka nan kuma kiran Sallah zai rika kai wa har cikin filin wasa.
Sannan an ware wajen sallah a kowane filin wasa tare da tanadar wadanda za su koyar da Sallah.