Qatar 2022: Zakir Naik na halartar Gasar Kofin Duniya
Gwamnatin Qatar ta gayyaci Dokta Zakir Naik domin ya gabatar da majalisin wa’azi a yayin da ake Gasar Cin Kofin Duniya a kasar.
Fitataccen mai wa’azin Musulunci dan kasar Indiya, Dokta Zakir Naik na halartar gasar kwallon kafar na Cin Kofin Duniya da za a soma a Qatar a ranar Lahadi.
Hakan ta bayyana ne bayan fitar hotunan Dokta Zakir Naik bayan saukarsa a filin jirgin sama na Doha, babban birnin kasar Qatar a ranar Asabar.
- Qatar 2022: Yau za a fara Gasar Cin Kofin Duniya
- Kiristoci biyar sun musulunta a wurin wa’azin Dokta Zakir Naik a Abuja
- Zakir Naik ya lashe kyautar Sarki Faisal kan hidima ga Musulunci
Wasu bayanai sun nuna cewa mai Zakir Naik ya je Qatar ne a bisa gayyatar gwamanatin kasar na ya gabatar da wani majalisin wa’azi a yayin da ake gasar.
Qatar ta bijiro da wasu tsare-tsare na yada addinin Musulunci a yayin gasar Cin Kofin Duniya da ake sa ran mutum sama da mutane miliyan biyu da rabi za su halarta.
Wasu daga cikin tsare-tsaren sun hada da samar da wuraren Sallah da kuma wuraren alwala a filayayen wasa, abin da ba a taba yi ba a tarihin gasar a duniya.
Qatar ta kuma hana sayar da barasa a wuraren da za a buga wasannin.