Qatar na ci gaba da tallafa wa Gaza

Qatar za ta ci gaba da tallafa wa ayyukan cigaba a Gaza da ke karkashin Hamas kamar yadda jakadan Katar ya sanar duk da cewa kasashen Larabawa na fushi da kasar saboda irin wannan tallafin da take bayar wa. Mohammed al-Amadi wanda shi ne shugaban kwamitin sake gina Gaza ya nanata alkawarin hakan ne a […]

Qatar na ci gaba da tallafa wa Gaza

Qatar za ta ci gaba da tallafa wa ayyukan cigaba a Gaza da ke karkashin Hamas kamar yadda jakadan Katar ya sanar duk da cewa kasashen Larabawa na fushi da kasar saboda irin wannan tallafin da take bayar wa.

Mohammed al-Amadi wanda shi ne shugaban kwamitin sake gina Gaza ya nanata alkawarin hakan ne a lokacin da sakataren harkokin kasar wajen Amurka Red Tillerson ya je yankin domin tattaunawa a kan rikicin day a dabaibaye yankin.

Idan ba a manta ba a watan da ta gabata ne kasashen Saudi Arabi Hadaddiyar Daular Larabawa da Egypt ta yanke alaka da kasar Qatar, inda suka zargi kasar da taimakon masu tsatstsauran ra’ayi  yankin wanda suka hada da Hamas, zargin da Qatar ta karyata.

“Na zo ne domin na tabbatar wa mutanen Falasdinawa cewa za mu ci gaba da ayyukan da muke yi kuma za mu fara sababbi,” kamar yadda al-Amadi ya fada a bikin kaddamar da gina wasu gidajen zama guda takwas. Sannan ya nanata cewa ziyarar ta zo a daidai lokacin da ake bukata.

Daya daga cikin manyan dalilin da yasa kasar Saudi Arabia da sauran kasashen Larabawa suka yanke alaka da kasar Qatar shi ne domin a tursasa musu su yanke alaka da kungiyar ‘yan uwa musulmai wadda it ace asalin kungiyar da ta haifar da ‘yan ta’addan Hamas.

Qatar ta kasance kasa ma fi tallafawa Gaza a shekara biyar da suka wuce, inda ta kasha fiye dalar Amurka 500 domin gina gidaje, asibitoci da kuma samar da ababen more rayuwa.

Al-Amadi ya nanata cewa kasarsa bat a tallafa wa Hamas, amma irin katafaren gine-ginen da suke yi ana ganin suna yi ne domin taimakon Hamas din. Sannan kuma manyan ’yan Hamas da ake nema suna boya a kasar ta Qatar.