Qatar ta samu makinta na farko a tarihin gasar Kofin Duniya
Ko da ba mu farke ƙwallon ba, hakan ba zai hana ni yin alfahari da yadda ’yan wasan suka yi ƙwazo ba, inji Lapotegui.
Ƙasar Qatar ta samu makinta na farko a tarihin gasar Kofin Duniya bayan da ta yi canjaras 1-1 da Switzerland a wasan farko da suka buga a ranar Asabar.
Switzerland ce ta fara cin ƙwallo tun a minti na 17 da soma wasan ta hannun ɗan wasanta, Breel Embolo, a bugun fenariti.
- Yau Lahadi za mu sanya hannu a yarjejeniya da Iran — Trump
- Za a yi jana’izar jagoran addinin Iran Ali Khamenei a watan Yuli
Sai dai Qatar ta yi ƙoƙarin dawo wa cikin wasan, inda ta samu nasarar farke ƙwallon rama a mintuna na ƙarshe bayan wani kuskure da ɗan bayan Switzerland, Miro Muheim, ya yi wanda ya jefa ƙwallo cikin ragar ƙasarsa.
Wannan ne karo na biyu da Qatar ke buga Gasar Kofin Duniya bayan ta karɓi baƙuncin gasar ta 2022, kuma wannan maki shi ne na farko da ta taɓa samu a tarihin gasar.
Kocin Qatar ɗan asalin Spain, Julen Lopetegui, ya bayyana farin ciki kan yadda ’yan wasansa suka nuna jajircewa duk da matsin lambar da suka fuskanta.
“Ko da ba mu samu nasarar farke ƙwallon ba, hakan ba zai hana ni yin alfahari da yadda ’yan wasan suka yi ƙwazo ba. Amma babban abin farin ciki shi ne mun samu sakamakon da ya zama tarihi,” in ji shi.
Switzerland ce ta fi garawa da kuma riƙe ƙwallo a wasan, inda ta yi yunƙurin kai hari sau 26 a ragar Qatar, amma ta kasa ƙara yawan ƙwallayenta.
A ƙarshe, kyaftin ɗin Qatar, Boualem Khoukhi, ya matsa wa masu tsaron baya lamba a lokacin da aka ƙara lokaci, lamarin da ya janyo Muheim ya zura ƙwallo a ragarsa a minti na 94.
A wasa na gaba, Switzerland za ta kara da ƙasar Bosnia and Herzegovina a Los Angeles, yayin da Qatar za ta kara da mai masaukin baki Canada a Vancouver.